Rajab
Rajab (Larabci رجي) shi ne wata na bakwai a cikin jerin watannin musulunci na shekara, Ma'anar Rajab na nufin "Kiyayewa". Wannan watan na cikin watanni hudu waɗanda haramun ne yin yaƙi a cikin su. Sannan yana cikin watannin da Allah yace nasa ne, yakanyi yafiya, rahama, rabon arziki a cikinsa.
Rajab | |
---|---|
calendar month (en) | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | sacred month (en) da watan Hijira |
Mabiyi | Jumada al-Thani |
Ta biyo baya | Sha'ban |
Anaso a yawaita ambaton Allah da neman afuwarsa a ciki, sannan a kiyaye yawan aikata ɓarna.
Ranakun tarihi
gyara sasheMusulmai sun yi Imani a watan Rajab ne aka haifi Sayyadina Aliyu a cikin Dakin Ka'aba. Ranar 7; Sufaye mabiya darikar Chishti suke bikin ranar Khawaja Moinuddin Chishti Ranar 27; Annabi Muhammad (s.a.w) ya yi mi'iraji. Ranar 28; Sayyadina Hussain ya fara tafiyarsa daga Madina zuwa Kufa
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.