Perpetua Ijeoma Nkwocha ,(an haife ta a ranar 3 watan Janairu shekarar 1976), 'Yar Najeriya ce, wacce kuma takasance shahararriyar yar'wasan ƙwallon ƙafa ce, kuma coach ɗin Clemensnäs IF a Swedish Women's Football Division 2, ta buga wasa ma ƙungiyar Swedish kulub Sunnanå SK. Ita mamba ce kuma mai riƙe da captain na ƙungiyar wasan kwallon kafa na mata Nigeria women's national football team.

Perpetua Nkwocha
Rayuwa
Haihuwa Lagos,, 3 ga Janairu, 1976 (48 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya1999-2015
Sunnanå SK (en) Fassara2004-2004
Pelican Stars F.C. (en) Fassara2005-2005
Sunnanå SK (en) Fassara2007-2014
Clemensnäs IF (en) Fassara2015-
 
Muƙami ko ƙwarewa Ataka
Lamban wasa 22
Tsayi 180 cm
Kyaututtuka
Perpetua Nkwocha

A matakin duniya

gyara sashe

Tare da ƙungiyar wasan Nigeria national team takasance ta buga gasar CAF Women's Championship har guda bakwai; (2002, 2004, 2006, 2008, 2010, 2012 da 2014), inda da ita aka lashe guda biyar daga cikinsu (2002, 2004, 2006, 2010 da 2014). A gasar 2004 African Women's Championship, taci ƙwallaye hudu a wasan karshe na gasar a wasan Najeriya da Cameroon inda ta taimaka wa kasar ta lashe gasar. Ta bar kafa tarihi a gasar inda taci ƙwallaye tara a gasar, kuma an bayyana ta mafi hazaƙa a gasar.[1] Nkwocha an sake bayyana ta amatsayin African Women's Footballer of the Year a shekarun 2004, 2005, 2010 da 2011 daga Confederation of African Football (CAF).

Har wayau Nkwocha takasance daga cikin FIFA Women's World Cup na shekarar (2003, 2007, 2011 da na 2015), da kuma kasancewa acikin Olympic tournaments na Sydney 2000, Athens 2004, da Beijing 2008.

Ƙyautuka

gyara sashe
Najeriya

Manazarta

gyara sashe