Ossai Nicholas Ossai ɗan siyasan Najeriya ne. Ya kasance memba mai wakiltar Ndokwa East/Ndokwa West/Ukwuani Federal Constituency a majalisar wakilai. [1] [2]

Ossai Nicholas Ossai
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

11 ga Yuni, 2019 -
District: Nkokwa East/Ndokwa West/Ukwuani
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

9 ga Yuni, 2015 - 9 ga Yuni, 2019
District: Nkokwa East/Ndokwa West/Ukwuani
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

6 ga Yuni, 2011 - 6 ga Yuni, 2015
District: Nkokwa East/Ndokwa West/Ukwuani
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Rayuwar farko da ilimi

gyara sashe

An haifi Ossai Nicholas Ossai a ranar 4 ga watan Nuwamba 1963 kuma ya fito daga jihar Delta. Yana da aure da 'ya'ya. Ya kammala karatunsa na firamare a Urban Community Primary School da ke Abakaliki, sannan a shekarar 1980 ya samu shaidar kammala karatunsa na farko (FSLC). Ya kammala karatun daga makarantar CMS Grammar School, Legas a shekarar 1988 sannan ya yi digiri na farko a shekarar 1997 a Jami'ar Najeriya, Nsukka. [2] [3] [4]

A shekarar 2011, an fara zaɓen sa a matsayin mamba mai wakiltar Ndokwa East/Ndokwa West/Ukwuani Federal Constituency. An sake zaɓen sa a shekarar 2015, sannan a shekarar 2019, inda ya zama ɗan majalisar tarayya a karo na uku a ƙarƙashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP). Nnamdi Ezechi ne ya gaje shi a shekarar 2023. [2] Ya yi aiki a matsayin shugaban, Kwalejin Ilimi, Agbor, Jihar Delta, kuma ya kasance ɗan majalisar dokokin jihar Delta. [4]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Legislator Details - ConsTrack Track and Report on Governement Funded Projects in Nigeria". constrack.ng. Retrieved 2024-12-27.
  2. 2.0 2.1 2.2 "Citizen Science Nigeria". citizensciencenigeria.org (in Turanci). Retrieved 2024-12-27. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":1" defined multiple times with different content
  3. Adeolu (2017-03-07). "OSSAI, Hon. Nicholas Ossai". Biographical Legacy and Research Foundation (in Turanci). Retrieved 2024-12-27.
  4. 4.0 4.1 "Hon. Nicholas Ossai biography, net worth, age, family, contact & picture". www.manpower.com.ng. Retrieved 2024-12-27. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":2" defined multiple times with different content