Olajumoke Okoya-Thomas
Olajumoke Abidemi Okoya-Thomas mamba ce a Majalisar Wakilan Tarayyar Najeriya.[1]Ta kasance 'yar jam'iyyar All Progressives Congress kuma tana wakiltar mazabar Lagos Island I Mazabar Tarayyar Lagos, Najeriya .[2]
Olajumoke Okoya-Thomas | |||
---|---|---|---|
3 ga Yuni, 2003 - | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | 20 ga Janairu, 1957 (67 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Harshen uwa | Yarbanci | ||
Ƴan uwa | |||
Mahaifi | Molade Okoya-Thomas | ||
Karatu | |||
Makaranta | Makarantar Kasuwanci ta Harvard. | ||
Harsuna |
Turanci Yarbanci Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa |
All Progressives Congress Alliance for Democracy (en) |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheTa kasance 'ya ga Cif Molade Okoya-Thomas,[3] Asoju Oba na Legas, an haife ta a ranar 20 ga Janairu 1957. Tana da difloma a fannin gudanar da Gwamnati (Senior Managers in Government) daga Jami'ar Harvard da difloma a sec. gudanarwa daga Kwalejin Burleigh.[4]
Harkar siyasa
gyara sasheOlajumoke Okoya-Thomas ta fara aiki ne a ranar 29 ga Afrilun 2011 a karo na uku a jere a majalisar wakilan tarayya. Ra'ayoyin ta na doka da shari'a sun ta'allaka ne akan cigaban zamantakewar Mata da Ƙananan yara.[5] A yanzu haka ita ce Shugabar kwamiti a kan Siyarwar Jama'a sannan kuma mamba ce a kwamitin "Banking & Currency, Diaspora, Niger Delta", da kuma kwamitin Mata a majalisa.
Ita ce tsohuwar shugabar kwamitin gidan yarin.[6]
Olajumoke Okoya-Thomas ta dauki nauyin kudirin doka kan tilasta shayar da jarirai nono a shekara ta 2013. Ƙudirin ya gaza saboda wakilan sun dage kan cewa batu ne da ya fi dacewa a bar shi a bainar jama'a saboda "babu macen da za a tilasta mata shayar da danta nono" duk da cewa sun amince da fa'idodin lafiya na shayar da nonon wanda ba a iya jayayya da hakan.[7] Har wayau, ita ce kuma shugabar mata na jam’iyyar All Progressive Congress a jihar Legas.[8]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Public offices held by Olajumoke Abidemi Okoya-Thomas in Nigeria". citizensciencenigeria.org. Retrieved 5 April 2022.
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2014-03-29. Retrieved 2020-11-22.
- ↑ "Jumoke Okoya Runs Into Political Trouble For Eyeing Remi Tinubu's Senatorial Seat!". Society Now Nigeria. Archived from the original on 31 March 2014. Retrieved 29 March 2014.
- ↑ "Olajumoke Okoya-Thomas". Nnu.ng - Nigeria News Update. Retrieved 22 February 2022.
- ↑ "OLAJUMOKE OKOYA-THOMAS Politician Profile Page". Shine Your Eye. Retrieved 29 March 2014
- ↑ "Members Federal House of Representatives". Nigerian National assembly. Retrieved 29 March 2014.
- ↑ "Reps Reject Bill On Exclusive Breast Feeding". Channels TV. 29 January 2013. Retrieved 29 March 2014.
- ↑ Admin. "Lagos APC: Jumoke Okoya-Thomas task party leaders on Kemi Nelson's conduct | National Daily Newspaper". Retrieved 27 August 2019.