Ofe Owerri

Ofe owerri yana daya daga cikin tsadar miya ta Gabashin Najeriya. Ana yin ta da nama iri -iri da kifi.Ofe owerri galibi ana yin sa ne yayin bukukuwa na musamman a yankin Gabashin Najeriya.

Ofe Owerri wani abincin kabilar Igbo ne a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya. Ana yin miya da katantanwa, naman Sa,nama iri-iri da kifi.

Ofe Owerri
Kayan haɗi Katantanwa, gishiri, nama, Manja, borkono, naman shanu da kifi
Tarihi
Asali Najeriya

Kamar yadda sunan ke nuna miya ta shahara a tsakanin mutanen da ke zaune a babban birnin jihar imo,Owerri.

Miyar tana daya daga cikin miyar Igbo mafi tsada shiyasa Ofe Owerri ta samu lakabin 'Jewel of South East'.

Ana amfani da kayan lambu iri-iri irin su okazi da leaf uziza wajen shirya kayan abinci na Igbo.Ugu na iya zama madadin uziza lokacin da ba ya samuwa.Sauran sinadaran sun haɗa da nau'in kifi daban-daban da nama da crayfish.Ana dafa Ofe Owerri da dabino sai aci a rika daka miya.

Sauran abinci

gyara sashe

Ana iya cin Ofe Owerri da semolina,fufu,dayan dawa da Eba.

Duba kuma

gyara sashe

Najeriya abinci

Owerri

na GACIOUS