Nuhu Bamalli Polytechnic
Nuhu Bamalli Polytechnic, makarantan jami'a ce ta ilimi da ke Zariya a Jihar Kaduna, Najeriya . Gwamnatin jihar Kaduna ta kirkiro ta da dabarun samar da kimiyya a fannonin ilimi na injiniyarin a ranar 2 ga Fabarelu a shekara na 1989 don samar da horo da dabarun ci gaba a fannin Injiniyarin, da amfani da kimiya, kasuwanci da sauran bangarorin ilmantarwa. Kwalejin ɗaya ce daga cikin makarantun koyar da abubuwa da dama Musamman a bangaren kimiya da injiniyarin datake mallakin gwamnatin jihar Kaduna. An sanya sunan wannan fasaha ta zamani ne bayan ministan harkokin waje na Najeriya Nuhu Bamalli
Nuhu Bamalli Polytechnic | |
---|---|
| |
Bayanai | |
Iri | cibiya ta koyarwa |
Ƙasa | Najeriya |
Harshen amfani | Turanci |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 2 ga Faburairu, 1989 |
Mazauni
gyara sasheBabbar harabar kwalejin ta zamani tana cikin tsohuwar UPE, a kan hanyar Kaduna-Zariya tare da ƙarin cibiyoyi a Tudun wada Gaskiya, da Samarun Kataf, a karamar hukumar Zangon Kataf na jihar Kaduna.
- Babban zangon ya hada da Makarantar koyon aikin Kimiyya, Injiniyarin, Nazari da Muhalli.
- Makarantar Gudanarwa da karatun farko suna Gaskiya, Tudun Wada Zariya
- Makarantar Fasaha ta Noma a Samarun Kataf, Kudancin Kaduna