'

Nokuthula Ledwaba
Rayuwa
Haihuwa Roodepoort (en) Fassara, 1983 (40/41 shekaru)
ƙasa Afirka ta kudu
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a jarumi, ɗan wasan kwaikwayo da television personality (en) Fassara
IMDb nm2745792


Nokuthula Ledwaba,' (an haife ta a shekara ta 1983), ƴar wasan kwaikwayo ce ta Afirka ta Kudu. An fi saninta da rawar da ta taka a cikin shahararrun jerin wasannin Rhythm City da The River.[1]

Rayuwa ta sirri

gyara sashe

An haife ta a shekara ta 1983 a yankin Mofolo a cikin Soweto, Afirka ta Kudu. Mahaifiyarta, Grace Vilakazi-Ledwaba ta haife ta tun tana ƙarama. Mahaifinta ya rasu shekaru 33 da suka wuce lokacin da mahaifiyarta ke da ciki. Da yake ta haifi ƴaƴa tun suna kanana, mahaifiyarta ta sha wahala wajen renon su. Don haka ta miƙa Nokuthala ga innarta. Ssannan ta girma a Soshanguve, Arewacin Pretoria tare da kawarta. Bayan ta zama budurwa, ta san danginta da kuma mahaifinta da ake kira Mavuso. Sai ta je ta ga mahaifiyarta ta zauna da ita. Duk da haka, mahaifiyarta ta rasu a watan Satumbar 2015.[2]

Fina-finai

gyara sashe
  • Hard Copy a matsayin Leah Gumede
  • Umlilo as Dumile Simelane / Dumile
  • Roots a matsayin Binta Kinte
  • Mandela: Long Walk to Freedom a matsayin Courthouse Young Woman
  • Mary and Martha as Micaela
  • Rhythm City as Tshidi Khuse
  • The River a matsayin Angelina
  • Abomama a matsayin Mapule
  • Ambitions a matsayin Thembi
  • Reyka a matsayin Portia

Manazarta

gyara sashe
  1. "5 Mins With Nokuthula Ledwaba". bona. 2020-11-21. Archived from the original on 2017-03-22. Retrieved 2020-11-21.
  2. "Nokuthula finds her roots and fulfilment". sowetanlive. 2020-11-21. Retrieved 2020-11-21.

Hanyoyin Hadi na

gyara sashe