Nathalie Yamb 'yar kasar Kamaru-Swisshiya ce kuma 'yar kasuwa. [1] [2] Ta shahara da adawa da ayyukan Faransa a Afirka wanda ita da wasu suka bayyana a matsayin mulkin mallaka. [3] [4] An haife ta a Switzerland kuma ta girma a Kamaru, sannan ta tafi jami'a a Jamus. [5] A cikin shekarun 2010, ta taimaka wajen tafiyar da jam'iyyar siyasa a Ivory Coast [1] Sai dai kuma an kore ta ne a shekarar 2019 ba tare da fuskantar shari'a ba bayan da ta soki gwamnatin Ivory Coast a wani taro a ƙasar Rasha. [3] Yamb ta samu goyon bayan oligarch na Rasha kuma shugaban haya Yevgeny Prigozhin kuma ta taimaka wajen yaɗa farfagandar Pro-Kremlin. [6] [7] Ƙaunar adawarta ta Faransa ta sa a cikin watan Janairu 2022 haramcin shiga da zama a ƙasar Faransa, wanda aka bayyana a cikin Oktoba 2022. [8] Yamb ta shiga a matsayin "mai sa ido na ƙasa da ƙasa mai zaman kansa" yayin zaɓen raba gardama na 2022 a Gabashin Ukraine. [9] [10]

Nathalie Yamb
Rayuwa
Haihuwa La Chaux-de-Fonds (en) Fassara, 22 ga Yuli, 1969 (54 shekaru)
ƙasa Switzerland
Kameru
Mazauni Switzerland
Kameru
Jamus
Ivory Coast
Switzerland
Karatu
Harsuna Faransanci
Turanci
Sana'a
Sana'a political activist (en) Fassara, ɗan kasuwa da video blogger (en) Fassara
Employers Maersk (en) Fassara  (2005 -  2007)
MTN Group (en) Fassara  (2007 -  2014)
Imani
Jam'iyar siyasa Liberty and Democracy for the Republic Party (en) Fassara
nathalieyamb.com

Manazarta gyara sashe

  1. 1.0 1.1 "Nathalie Yamb". Roscongress Foundation. Retrieved 2021-03-24.
  2. Conzett, Anja (2021-06-24). ""Staatliche Entwicklungshilfe – schafft sie ab!"". Republik (in Jamusanci).
  3. 3.0 3.1 "Swiss-Cameroonian activist deported to Switzerland". SWI swissinfo.ch (in Turanci). 2019-12-03. Retrieved 2021-03-24.
  4. Publisher, A. M. C. (2023-05-05). "Nathalie Yamb: The activist fighting France's presence in the African continent". AMC (in Turanci). Retrieved 2023-05-05.
  5. "Nathalie Yamb : "Ma mère est une battante, elle est ma référence "". Actu Cameroun (in Faransanci). 2020-01-11. Retrieved 2021-03-24.
  6. https://www.lemonde.fr/en/le-monde-africa/article/2023/08/06/the-faces-of-russia-s-influence-across-the-african-continent_6082513_124.html
  7. https://www.state.gov/disarming-disinformation/yevgeniy-prigozhins-africa-wide-disinformation-campaign/
  8. "La France informe Nathalie Yamb de son interdiction d'entrée et de séjour sur le territoire national". rfi (in Faransanci).
  9. https://rusieurope.eu/hidden-in-plain-sight-pro-kremlin-pan-african-influencers-and-the-threat-to-africa-s-stability-and-democracy/
  10. https://www.ukrinform.net/rubric-society/3766407-putins-friends-and-prigozhins-network-foreign-observers-in-pseudo-elections-in-occupied-areas.html