Nancy Illoh yar jarida ce a Najeriya, Ita ce mai gabatar da shirin MoneyShow.[1] a gidan Talabijin na Afirka mai zaman kansa, sannan kuma mai ba da shawara akan harkokin yada labarai, kuma Manajan Channel na Tashar Kasuwancin Afirka a Daarsat.[2] Ita ce Babbar Jami'i a Majalisar Tattalin Arzikin Afirka. kuma ta gudanar da shirye shirye a gidajen talabijin daban-daban.[3]

Nancy Illoh
Rayuwa
Sana'a
Sana'a ɗan jarida

Rayuwa da ilimi gyara sashe

Illoh yar asalin jihar Delta ce kuma yar fari a cikin yara shidan da iyayen su suka haifa. Amma an haife ta ne a Jihar Legas, Najeriya inda ta yi karatun boko tun kafin ta ci gaba zuwa Jami’ar Nnamdi Azikiwe, Awka inda ta yi BSc. a ilimin kimiyyar lissafi da ilimin halittu.[4]

Ayyuka gyara sashe

Nancy Illoh mai watsa shirye-shirye ce, mai gabatar da shirye shirye, kuma furodusa ce wacce ke hada shirye shirye, da kuma kafa tushen tattalin arzikin na talabijin, wanda aka nuna a Najeriya da Nahiyar Afirka .

A cikin shekarar 2007, ta zama wani ɓangare na ƙungiyar MoneyShow, wanda wani shiri ne a kan AIT inda ake tattaunawa akan harkan kasuwanci da mu'amalar kuɗi, ta hanyar gayyato mutanen Afirka. Ita da tawagar ta sun yi hira da tsohon shugaban bankin bunkasa Afirka Donald Kaberuka, Farfesa John Kuffor, tsohon shugaban kasar Ghana, Adams Oshiomhole da Sanusi Lamido Sanusi da dai sauransu.[5][6]

Duk dayake Illoh dalibar kimiyya ce, amma ta sami sha'awar zane-zane lokacin da tayi rubuce rubuce, kuma ta jagoranci wasan kwaikwayo akan wayar da kai kan HIV yayin da take makarantar sakandare. Daga baya ta shiga gidan Talabijin na jihar Delta, tana gabatar da shiri, da kuma kafa shirye-shirye daban-daban a matsayin dalibar jami'a. Ta shiga NTA ne a lokacin da take aikin NYSC don tara kwarewa da fallasawa.

An karrama ta da babban matsayi na Adã Né kwùlí Ùwáa daga mai martaba sarkin Obi Jideuwa, Sarkin Issele Azagba, Aniocha ta Arewa a jihar Delta .[7][8]

Rayuwar ta gyara sashe

Yar asalin jihar Delta ce.[9]

Manazarta gyara sashe

  1. https://www.vanguardngr.com/2020/03/nepc-pdf-ii-boost-non-oil-export/
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-05-01. Retrieved 2020-11-14.
  3. https://punchng.com/economic-adviser-shehu-sani-disagree-on-border-closure/
  4. http://biography.hi7.co/biography-of-nancy-illoh--producer-tv-presenter--56651dc415e91.html
  5. https://moneylinewithnancy.com/
  6. https://theeagleonline.com.ng/edo-pdp-candidate-was-detained-for-three-months-for-financial-misconduct-oshiomhole/
  7. https://www.cknnigeria.com/2018/12/ait-presenter-nancy-illoh-bags.html
  8. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-05-21. Retrieved 2021-05-21.
  9. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-03-01. Retrieved 2020-11-14.