Nair Filipe Pires de Almeida (an haife ta a ranar 23, ga watan Janairu shekara ta 1984 a Lobito, lardin Benguela ), 'yar wasan ƙwallon hannu ce ta Angola mai ritaya. Almeida ta fara aikinta a wata karamar kungiyar kwallon hannu mai suna Escola de Andebol da Restinga, do Lobito (EARL). [1] Ta yi takara a gasar Olympics ta bazara a 2004 a Athens da kuma gasar cin kofin duniya ta shekarar 2005.[2] A gasar cin kofin duniya ta 2007 Angola ta zama ta 7, yayin da Almeida ta zura kwallaye 57 kuma ita ce ta shida a jerin ‘yan wasan da suka fi zura kwallaye. Ta taka leda a kasar Angola a gasar Olympics ta bazara a shekarar 2008 da aka yi a birnin Beijing da kuma gasar lokacin rani ta shekarar 2012 da aka yi a birnin London. [1]

Nair Almeida
Rayuwa
Haihuwa Lobito, 23 ga Janairu, 1984 (40 shekaru)
ƙasa Angola
Karatu
Harsuna Portuguese language
Sana'a
Sana'a handball player (en) Fassara
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru GP G
Clube Desportivo Primeiro de Agosto (en) Fassara-
 
Tsayi 181 cm

Manazarta gyara sashe

  1. 1.0 1.1 Athlete Biography – De ALMEIDA Nair Filipe PiresBeijing 2008 Olympics (Retrieved on 4 December 2008)
  2. Hilary; Gjerde, Arild; Heijmans, Jeroen; Mallon, Bill ; et al. " Nair Almeida Olympic Results" . Olympics at Sports-Reference.com . Sports Reference LLC. Archived from the original on 18 April 2020. Retrieved 13 August 2017.

Hanyoyin haɗi na waje gyara sashe

  • Nair Almeida at Olympedia