Mutanen Mossi

kabila a Burkina Faso da Togo

Mossi itace ƙabilar Gur 'yan asalin kasar Burkina faso ta zamani, wanda sukazo asali daga Kogin Volta. Mossi sune mafi girman kabilla a Burkina Faso, wanda ya zama kashi 52% na yawan jama'ar kasar , ko kuma kimanin mutane miliyan 11.1. Sauran kashi 48% na yawan mutanen Burkina Faso sun hada da kabilu sama da 60, galibi daga Gurunsi, Senufo, Lobi, Bobo, Bissa da Fulani. Mossi suna magana da yaren Mòoré.[1]

Mutanen Mossi

Yankuna masu yawan jama'a
Burkina Faso, Ghana, Mali da Togo

Mutanen Mossi sun samo asali ne daga kasar Burkina Faso, kodayake yawancin mutanen suna zaune a kasashe makwabta, kamar kasar Benin, Côte d'Ivoire, Ghana, Mali, da Togo. A shekarar 2022, ƙididdigar yawan mutanen Burkina Faso ya kasance sama da miliyan 20, kuma sama da 11M daga cikinsu yan Mossi ne. Sauran mutanen Mossi miliyan 2 suna zaune a Côte d'Ivoire.

A yadda tarihinsu yake Mossi sun fito ne daga asalin auren auren yarima Dagomba, Yennenga, da sarauniyar dagomba na Mandé. wanda sun kasance mafarauta.

Yennenga yar sarauniya ce, 'yar sarki Dagbon na arewacin Ghana na yanzu. a yanzu haka Kabarin Gbewaa yana cikin Pusiga a yankin kudancin Ghana . Labari ya nuna cewa yayin da zagaya masarautunta a kan doki, ta bace hanya a inda mafarauci Rialé, ya cece ta. Sun yi aure kuma sun haifi ɗa, Ouedraogo, wanda aka san shi a matsayin asalimutanen Mossi.[2]

Bayani na gaba ɗaya

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe
  1. Roy, Christopher D. (August 18, 2006). "Burkina Faso". Art and Life in Africa Project. University of Iowa. Archived from the original on November 25, 2009. Retrieved February 11, 2010.
  2. Debutify. "The Rise & Fall of The Powerful Mossi Kingdoms". Our Ancestories (in Turanci). Retrieved 2022-04-25.