Mustapha Filali
Mustapha Zakariyya,( Larabci: مصطفى الفيلالي 5 ga watan Yuli 1921 - 20 Janairu shekarar 2019) ɗan siyasan Tunusiya ne. Shi ne Ministan Noma na Tunusiya na farko bayan yasamu 'yancin kai. ya kasan ce minista ne na nadaya a kasar Tunusiya.
Mustapha Filali | |||
---|---|---|---|
15 ga Afirilu, 1956 - 1 Oktoba 1957 | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Nasrallah (en) , 5 ga Yuli, 1921 | ||
ƙasa |
French protectorate of Tunisia (en) Tunisiya | ||
Mutuwa | 20 ga Janairu, 2019 | ||
Ƴan uwa | |||
Yara |
view
| ||
Karatu | |||
Makaranta |
Sadiki College (en) Faculty of Arts of Paris (en) | ||
Harsuna |
Larabci Faransanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa da trade unionist (en) | ||
Kyaututtuka | |||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa |
Neo Destour (en) Socialist Destourian Party (en) |
Tarihin rayuwa
gyara sasheFilali yayi karatu ne a Kwalejin Sadiki dake Faculté des lettres de Paris, inda ya sami digirinsa na biyu a cikin adabin larabci. Bayan karatunsa,a Filali ya yi aiki a matsayin malamin adabi a makarantun firamare da sakandare a Tunisia . Ya kasance mai matukar aiki a kungiyar Kwadago ta Tunusiya (UGTT), inda ya yi aiki don inganta tattalin arzikin Sfax .
Saboda goyon bayan da UGTT ta yi wa Habib Bourguiba, an nada Filali ne a matsayin ministan aikin gona da zarar Bourguiba ya sami iko a matsayin shugaban Tunisia na daya mai yancin kansa a 1956. A matsayinsa na minista, Filali ya yi aiki don kawo karshen cin mutunci . Daga nan aka nada Filali a matsayin ministan yada labarai. Koyaya, zai bar gwamnati a ranar 30 ga watan Disamba 1958. Zai jagoranci Jam'iyyar Socialist Destourian daga 26 ga watan Oktoba zuwa 31 ga watan Oktoba 1971. Bayan juyin juya halin Tunusiya na 2011, Filali ya kasance memba ne na Babban Hukuma don Tabbatar da Manufofinsa na Juyin Juya Hali, Gyara Siyasa da Canjin Dimokiradiyya .
Baya ga aikin siyasa, Filali ya kasance shugaban ofishin Maghreb na Kungiyar Kwadago ta Duniya a Algeria . Ya kuma kasance a cikin kwamitin gudanarwa na Cibiyar Nazarin Hadin Kan Larabawa a Beirut .
Kyaututtuka
gyara sashe- Babban Jami'in Dokar 'Yancin Kan Tunusiya (1966)
- Babban Jami'in Umurnin Jamhuriyar Tunisia (1968)
- Lambar Shugaban Algeria (2013)
Ayyuka
gyara sashe- Musulunci da sabon tsarin tattalin arzikin duniya (الإسلام و النظام الاقتصادي الدولي الجديد)
- Maghreb: kiran na gaba (المغرب العربي الكبير: نداء المستقبل)
- Teburin Inchirah (موائد الانشراح)