Musa Dattijo Muhammad
Musa Dattijo Muhammad OFR (An haife shi 27 ga Oktoba 1953) masanin shari'a ne na Najeriya kuma Kotun Koli ta Najeriya.[1]
Musa Dattijo Muhammad | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Chanchaga, 27 Oktoba 1953 (71 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta |
University of Warwick (en) Jami'ar Ahmadu Bello Jami'ar Bayero |
Sana'a | |
Sana'a | mai shari'a |
Rayuwar farko
gyara sasheAn haifi Musa Dattijo a ranar 27 ga Oktoba 1953 a Chanchaga, karamar hukumar Minna, babban birnin jihar Neja, a arewa ta tsakiyar Najeriya . Ya halarci makarantar Primary School da ke Minna da Sardauna memorial secondary inda ya samu shaidar kammala makarantar sakandare ta yammacin Afirka a shekarar 1971. Ya halarci Jami’ar Bayero da ke Jihar Kano a Arewacin Najeriya inda ya samu takardar shaidar kammala digiri kafin ya wuce Jami’ar Ahmadu Bello inda ya sami digiri na farko a fannin Shari’a a shekarar 1976. Daga baya ya sami digiri na biyu a fannin shari'a daga Jami'ar Warwick a shekarar1983. [2]
Shashin Shari'a
gyara sasheA watan Yulin 2012, an nada shi shugaban kotun kolin Najeriya a matsayin mai shari'a. Ya jagoranci hukuncin kotun koli da ta tabbatar da Gbenga Kaka a matsayin zababben Sanata mai wakiltar Ogun ta Gabas a zaben sanata na 2 ga Afrilu 2011. [3]
Memba na Kungiyoyi
gyara sashe- Memba na
- Kungiyar Lauyoyin Najeriya
- Memba Na, Ƙungiyar Lauyoyin Duniya
- Memba na, Kungiyar Benchers ta Najeriya