Marigayi Alhaji Musa Dankwairo zai ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin mawakan da darajarsu a idon duniya take ƙara haɓaka a al'ummar hausawa ,sai dai girmamawar bata tsaya iyaka nan ba domin kuwa manazarta a duniya suna ci gaba da amfanuwa da gudunmawarsa wadda ya baiwa fagen Ilimi, musamman farfesoshi da masu binciken ilimi a kan Yaren Hausa da ke nazari a jami'o'in Najeriya da June gabannan, Wani malami na jami'ar Usmanu Danfodio da ke Sokoto, Farfesa A.M Bunza ya bayyana cewa, an haifi marigayi musa dankwairo ne a shekara ta 1907, a garin Bakura na jihar Zamfara, wanda ke tsakanin jihar Zamfara da Sokoto da kimanin kilomita 105.

Musa Dankwairo
Rayuwa
Haihuwa 1907
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Mutuwa 1991
Sana'a
Sana'a mawaƙi

Tarihin Rayuwar Sa Data waqarsa

gyara sashe

Sunan Mahaifinsa Usman Dankwanda, ya rayu a garin Kaya da ke karkashin karamar hukumar Maradun, inda yake yiwa Sarkin Kayan Maradun waka a fadarsa. Mahaifin Dankwairo da kakansa duk makadan Sarkin Kayan Maradun ne. Musa Dankwairo Ya tashi ya tarar da kakansa da mahaifinsa suna waka a tare, amma ya fi rayuwa da mahaifinsa rayuwa ta hakika, to kuma tun yana dan shekaru 6 zuwa 7 ya fara fita inda mahaifinsa ke zuwa da shi cikin tsangaya ta waka. Bayan rasuwar mahaifinsa, sai ragamar kungiyar waka ta koma hannun Aliyu Kurna, wanda yaya ne ga Dankwairo, inda aka zabi Dankwairo ya zamto mataimakin Aliyu Kurna, wanda idan bayanan sai Dankwairo ya wakilce shi a matsayin shugaban tawagar ta mawaka.

Marigayi Alhaji Musa Dankwairo ya samu wannan lakabi na 'Dankwairo' tun lokacin mahaifinsa na raye. Mahaifinsa ya na da wani Yaro da ake kira Dankwairo saboda zakin muryarsa da kuma kwarewa wajen yin waka da iya farawa,sai Musa Dankwairo ya rinka kwaikwayon sa tare da kwaikwayon muryarsa, ganin cewa Musa ya kware kamar shi Dankwairon na asali sai ake kiransa da wannan lakabi na 'Dankwairo'. Tun daga wannan lokacin ne kuma Dankwairo ya fara shahara a fagen waka, wanda hakan ya sanya ya zamto mawaki ga marigayi Sardaunan Sokoto, Alhaji Ahmadu Bello, inda Dankwairo ya rera masa wakarsa ta farko mai taken 'Mai Dubun Nasara Garnaki Sardauna'. Marigayi Sardauna ya fifita tawagar Dankwairo fiye da kowace kungiyar mawaka, inda ya maida Dankwairo mawakin fadarsa tare da kyautatawa ta wuce misali wanda a wancan lokaci hankali baya kaiwa ga irin kyaututtukan da Sardauna Sokoto ya rinka yiwa Dankwairo da 'yan tawagarsa, kama daga sutura zuwa motar hawa.

A takaice dai, Musa Dankwairo ya yiwa Sardauna wakoki guda 17,kuma musabbabin saduwarsa da Sardauna kuwa a fagen siyasar NPC (Nothern People's Congress)da hausa majalissar mutanen arewa ne suka hadu, kasancewar Sardauna dan Siyasa ne kuma Basarake,saboda haka kuma yana bukatar mawakin sarauta da zai zauna tare da shi a fadarsa domin dabbaka sunan sa. Bayan rasuwar Sardauna a shekarar 1966,tawagar Dankwairo ta kwanta dama har na wani lokaci mai tsawo kafin ta ci gaba da wakokin yabo ga wasu sarakunan gargajiyar da suka shahara irin su; Sarkin Daura Bashar, Sultan na Sokoto da Sarkin Zazzau Aminu. Cikin shekaru 29 zuwa 30 da suka gabata, wa'adi na rayuwa ya riski marigayi Musa Dankwairo, inda ya bar 'ya'ya 14, maza 7 da mata 7, tare da jikoki 104 a yayin muturwarsa, wanda sun ci gaba da hayayyafa kamar yadda babban dan sa; Alhaji Garba Musa Dankwairo ya bayyana.

Manazarta

gyara sashe