Mukarama Abdulai
Mukarama Abdulai (an haife ta a ranar 16 ga Oktoba, shekarar 2002) 'yar wasan ƙwallon ƙafa ce ta ƙasar Ghana wadda ke taka leda a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Back Maideins da kuma ƙungiyar ƙwallon kafa ta mata ta ƙasar Ghana .
Mukarama Abdulai | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Tamale, 10 Oktoba 2002 (22 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Ghana | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Makaranta |
Jami'ar Nazarin Ci Gaban Tyler Junior College (en) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna | Turanci | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Mahalarcin
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Ataka | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 1.6 m |
Ta jagoranci kungiyar kwallon kafa ta Ghana a lokacin gasar cin kofin duniya ta mata 'yan kasa da shekaru 17 na shekarar 2018 a Uruguay, inda ta lashe kyautar takalmin zinare saboda kwallaye bakwai da ta ci a gasar. Ta ci kwallaye uku a wasa ɗaya a yayin karawar su ta farko da kasar da ta karbi bakuncin gasar. Bugu da kari, ta lashe Bronze Ball.
Lambobin Yabo
gyara sasheGasar kofin duniya na mata 'yan ƙasa da shekaru 17 na FIFA
- Ta samu kyautar takalmin zinare a gasar kofin duniya na FIFA na kwallon kafa na mata 'yan kasa da shekaru 17 [2018]
- A gasar cin kofin duniya na shekarar FIFA na kwallon kafa na mata 'yan kasa da shekaru 17 na shekarar 2018 ta samu Bronze Ball.
Manazarta
gyara sashe
Hanyoyin haɗin waje
gyara sashe- Mukarama Abdulai at Soccerway