Sarki Alhaji Muhammadu Dikko kuma anfi sanin sa da Muhammad Dikko ɗan Gidado CBE (1865 – May 1944)[1], ya kasance Sarkin Katsina ne na 47th, wanda ya yi mulki daga 9 ga watan Nuwamba shekara ta, 1906 har zuwa rasuwarsa a shekara ta, 1944. Shine sarkin Katsina na tara (9) a bangaren Fulani[1].

Muhammadu Dikko
Rayuwa
Haihuwa 1865
ƙasa Najeriya
Mutuwa 1944
Makwanci Jihar Katsina
Sana'a
Imani
Addini Musulunci

Tarihin rayuwa gyara sashe

An haife shi a shekara ta, 1865[2], a lokacin Sarki Muhammadu Bello, an naɗa shi sarauta lokacin yana da shekara ashirin da biyu (22) da haihuwa[1].

An naɗashi Durbi daidai lokacin yaƙin Basasar Kano. A lokacin da Lord Lugard ya shiga garin katsina, Dikko yana matsayin Durbin Katsina kuma an bashi alhakin kula da Turawa, cinsu da shan su, ƙibarsu da ramar su na hannunsa kamar yadda kuma sarkin lokacin watau Sarki Abubakar ya umurceshi[3].

Tarihi ya nuna cewa lokacin da aka naɗa sarki muhammad Dikko yana Gobir don siyayyar Raƙuma na Sarki Abubakar na lokacin daga nan aka tura masa takarda ya dawo, akan hanya ya haɗu da ɗan aike (mallam Giɗaɗo) daga liman wazirin katsina Haruna, cewa an kama Sarki Yero, an kuma naɗa shi sarki[4].

Da isowar bariki joji yace “Gwamna ya aiko, kaine Sarki” daga nan ya kama sarautar katsina[4].

Tafiye Tafiye gyara sashe

Sarki Muhammadu Dikko yana daya daga cikin sarakunan da suka fi kowa tafiye-tafiye zuwa qasashen qetare[4]. Daga lokacin da sarki zai je garin Makkah, Gwamna lugard ya haɗashi da soja mai suna “Mr. Wafaster” (webster) ya rakashi har Makka ya tashi katsina ranar talatin ga watan biyar a shekara ta, 1920, sannan ya isa birnin landan a biyar ga watan Bakwai a shekara ta, 1920. Sarkin ingila Nelo ya bashi lambar girma (Kings Medal for African Chiefs) a ranar 29 ga watan 7 a shekara ta, 1920, ya isa jidda wanda sharifin Makka Usaini ya amshe su, ya kare aikin hajji a ranar 12 ga watan 9 a shekara ta, 1920. Sannan ya fara biyawa ta ingila sannan ya dawo katsina a ranar 22 ga watan nuwamba a shekara ta, 1920[5].

A shekara ta, 1924, Sarki Dikko ya ƙara komawa Ingila don halartar taron nuna kayan ciniki na ƙasashen Ingila (Empire Exhibition).[5]Sarki ya ƙara komawa aikin hajji a shekarar, 1933 inda ya sake biyawa ta turai a shekarar, 1937 ya sake komawa Turai don ayi masa maganin idonsa dake ciwo[6].

Harkokin Wasanni gyara sashe

Duk wanda yasan Sarki Muhammadu Dikko yasanshi da son wasanni na motsa jini musamman wasan dawaki na polo. An kuma fara wasan dawaki watau Polo a katsina a shekarar, 1921, sannan mafi yawanci wanda suka buga wasan ƴa’ƴan sarki ne, da ƴa’ƴan hakimai, da ƴa’ƴan Wazirai. Kuma sarki ya kafa ƙungiyar kwallo da ake kira “katsina polo club”[7].

Gwanayen polo a katsina sun haɗa da;

-        Usman Nagoggo                                               (6)

-        Alhaji Ibrahim Galadiman Magani               (4)

-        Alhaji Yusuf                                                        (3)

-        Ɗan Dada                                                           (3)

Wanda ake kiran wannan lambobi “ Nigerian Polo Association Handicape[8]

Noma gyara sashe

Sarki Muhammadu Dikko ya kula da sha’anin Noma sosai wanda har alƙalin zazzau, Mallam Ahmadu Lugge, ya kanyi masa kirari da “Sahibul Harakaati Wal garaasati”[9].

Rasuwar Sarki gyara sashe

Sarki Muhammadu Dikko ya rasu a watan Fabrairu shekarar, 1944, bayan yayi jinya na kusan wata uku[10].

Hotuna gyara sashe

Bibiliyo gyara sashe

Burji, Badamasi Shu'aibu G., 1968- (1997).Gaskiya nagartar namiji : tarihin rayuwar Janar Hassan Usman Katsina. Kano: Burji Publishers.ISBN 978-135-051-2. OCLC 43147940.

Sani Abubakar Lugga, 1950- (2006). Dikko dynasty : 100 years of the Sullubawa ruling house of Katsina, 1906-2006. Katsina, Nigeria: Lugga Press. ISBN 978-978-2105-20-2. OCLC 137997519.

Manazarta gyara sashe

  1. 1.0 1.1 1.2 Burji, Badamasi Shu'aibu G., 1968- (1997).Gaskiya nagartar namiji : tarihin rayuwar Janar Hassan Usman Katsina. Kano: Burji Publishers. p.14. ISBN 978-135-051-2.
  2. Sani Abubakar Lugga, 1950- (2006). Dikko dynasty : 100 years of the Sullubawa ruling house of Katsina, 1906-2006. Katsina, Nigeria: Lugga Press. p.2. ISBN 978-978-2105-20-2.
  3. Burji, Badamasi Shu'aibu G., 1968- (1997).Gaskiya nagartar namiji : tarihin rayuwar Janar Hassan Usman Katsina. Kano: Burji Publishers. p.15. ISBN 978-135-051-2.
  4. 4.0 4.1 4.2 Burji,Badamasi Shu'aibu G., 1968- (1997).Gaskiya nagartar namiji : tarihin rayuwar Janar Hassan Usman Katsina. Kano: Burji Publishers. p.16. ISBN 978-135-051-2.
  5. 5.0 5.1 Burji, Badamasi Shu'aibu G., 1968- (1997).Gaskiya nagartar namiji : tarihin rayuwar Janar Hassan Usman Katsina. Kano: Burji Publishers. p.16-17. ISBN 978-135-051-2.
  6. Burji, Badamasi Shu'aibu G., 1968- (1997).Gaskiya nagartar namiji : tarihin rayuwar Janar Hassan Usman Katsina. Kano: Burji Publishers. p.17. ISBN 978-135-051-2.
  7. Burji, Badamasi Shu'aibu G., 1968- (1997).Gaskiya nagartar namiji : tarihin rayuwar Janar Hassan Usman Katsina. Kano: Burji Publishers. p.19. ISBN 978-135-051-2.
  8. Burji, Badamasi Shu'aibu G., 1968- (1997).Gaskiya nagartar namiji : tarihin rayuwar Janar Hassan Usman Katsina. Kano: Burji Publishers. p.20. ISBN 978-135-051-2.
  9. Burji, Badamasi Shu'aibu G., 1968- (1997).Gaskiya nagartar namiji : tarihin rayuwar Janar Hassan Usman Katsina. Kano: Burji Publishers. p.22. ISBN 978-135-051-2.
  10. Burji, Badamasi Shu'aibu G., 1968- (1997).Gaskiya nagartar namiji :tarihin rayuwar Janar Hassan Usman Katsina. Kano: Burji Publishers. p.28. ISBN 978-135-051-2.

Hanyoyin haɗin waje gyara sashe