Muhammad Kabir Nuhu-Koko
Rayuwa
Haihuwa Birnin, Kebbi, 16 ga Janairu, 1959 (65 shekaru)
Sana'a
Sana'a injiniya da civil servant (en) Fassara

Muhammad Kabir Nuhu-Koko, wanda aka fi sani da Kabiru Nuhu-Koko, ko MK Nuhu-Koko, ya kasance injiniyan gine-gine ne a Najeriya, kuma ma'aikacin gwamnati wanda ya yi aiki a ma'aikatar ayyuka ta tarayya a Legas daga 1984-1989. Daga nan ya koma babban bankin Nijeriya a shekarar 1990, ya kuma zama mataimakin darakta a sashen saye da sayarwa har ya yi ritaya a shekarar 2019. Nuhu-koko ya kuma kasance shugaban kungiyar tsofaffin dalibai na Unity Schools (USOSA) daga 2013 zuwa 2015.

Tarihin Rayuwa

gyara sashe

An haifi Nuhu-koko a Birnin Kebbi, Jihar Kebbi Najeriya daga cikin Iyalan Marigayi Alhaji Nuhu Balarabe Koko, fitaccen malami, kuma tsohon sakatare na dindindin a ma'aikatar ilimi ta jihar Sakkwatto. A lokacin ƙuruciyarsa, danginsa sun yi ƙaura daga wurare daban-daban saboda yanayin aikin koyarwar mahaifinsa.

Ilimi na farko

gyara sashe

Nuhu-koko ya halarci makarantar firamare ta Turaki a jihar Sakkwato 1972-1977.

Sakandare da ilimin gaba da sakandare

gyara sashe

Ya shiga Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Kano a shekarar 1977, sannan ya wuce babbar Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Ya kammala karatunsa na digiri (B.Sc) a fannin Gine-gine a shekarar 1983. sannan ya samu digiri na biyu (M.Sc.) a fannin Fasahar Gine-gine a shekarar 1988.

Nuhu-koko ya fara aikinsa ne a matsayin Injiniyan gine-gine a lokacin da yake aiki da Hukumar Raya Kogin Neja (NRBDA) Ilorin, wannan wani bangare ne na aikin matasa masu Yiwa Kasa Hidima (NYSC) 1983-1984. Ya ci gaba da aiki da ma’aikatar ayyuka ta tarayya Legas, a matsayin karamin ma’aikacin injiniya daga 1984-1989. A lokacin da yake a ma’aikatar ayyuka ta tarayya da ke Legas, ya yi wani gagarumin gwaji da ya kafa tushen rahoton ‘Amfanin da kwanson kwakwar manja wurin yin kankare’, wanda ya gabatar a Taron shekara-shekara na gwaji da sarrafa kayayyaki karo na 21. da yin Bincike a 1990. Yana daga cikin karatun digirinsa na biyu, kuma an yi magana da shi sosai a makarantun Najeriya. Ya fara aiki a babban bankin Najeriya a shekarar 1990, aikin da yasa shi komawa babban birnin tarayya, Abuja . Nuhu-koko ya ci gaba da aiki a bankin CBN inda ya shafe shekaru 30 yana gudanar da ayyukansa, ya kuma kula da wasu ayyukan gine-gine na bankin. Daga karshe ya kai matsayin shugaban sashen tsare-tsare, da aiwatar da ayyuka, saya da saida kadarorin da tallafi na bankin CBN. Sashen bankin da ke kula da duk manyan kwangiloli, saye da sayar da kadarori, kwangila da ayyukan gine-gine. Ya karbi wannan mukamin ne daga hannun mataimakin gwamnan na yanzu Edward Adamu, wanda daga nan ne aka kara masa girma zuwa mukamin Darakta, sashen kula da ma’aikata.

A shekarar 2013, Nuhu-koko ya tsaya takarar shugabancin kungiyar tsoffin daliban makarantar Unity School (USOSA) kuma ya yi nasara. Ya kasance Shugaban USOSA daga 2013-2015. A matsayinsa na Shugaban USOSA ya himmatu wajen ba da himma don ƙarin kudade na kwalejojin Gwamnatin Tarayya (Makarantar Unity) yana nuna rashin jin daɗinsa game da ruɓewar makarantun, tare da ayyana yaƙin gabaɗaya ga duk wanda yake so a soke su. Ya kuma jajirce wajen samar da isasshen tsaro ga makarantun hadin kai, musamman wadanda ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, inda rikicin ‘yan tada kayar baya ya lakume rayukan mutane da dama ciki har da dalibai.

  • Center of Excellence - University of Ibadan
  • Center of Excellence - University of Nigeria, Nsukka.
  • Center of Excellence - Ahmadu Bello University, Zaria

A ranar 20 ga watan Agusta, 2013, yayin da ya wakilci tsohon gwamnan babban bankin Najeriya , Sanusi Lamido Sanusi, Nuhu-koko ya gabatar da kudi naira biliyan 10 a matsayin kudaden shiga tsakani ga jami'ar Usman Dan Fodio, Sakkwato. Ya bayyana kudaden a matsayin wani bangare ne na CBN na CSR da nufin gina ababen more rayuwa, iyakarf aiki da ma’aikata ga jami’ar. Da yake jawabi ga manema labarai, ya ce;

 

Kyaututtuka da karramawa

gyara sashe

A ranar 31 ga watan Janairun 2016 ne kungiyar matasan Arewa ta karrama Nuhu-Koko da lambar yabo ta Sir Alhaji Ahmadu Bello Sardaunan Platinum Leadership Award. Haka kuma shi ne wanda ya samu lambar yabo ta Najeriya Arise Merit Award 2013 don 'Uplifting Nigerian Educational Standard'. Alhaji Nuhu-Koko kuma yana rike da sarautar 'Shettiman Koko' a mahaifarsa ta Koko .

Rayuwarsa

gyara sashe

Ya auri marigayi Rabi Abdu Gusau (Diyar Alhaji Abdu Gusau ) kuma sun haifi 'ya'ya 3 tare. Nuhu-Koko ya sake yin aure a shekarar 1996 ga Hadiza Nuhu-koko, yanzu haka yana da ‘ya’ya 5 da jikoki 4.

Duba kuma

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe