Moses Godia Shipi (an haife shi 2 ga watan Maris, shekara ta alif ɗari tara da saba'in da tara 1979A.c) ɗan kasuwa Najeriya ne kuma ɗan siyasa. Ya taɓa zama mataimaki na musamman ga tsohon gwamnan jihar Bauchi Alh. (Dr) Malam Isa Yuguda. An zaɓe a matsayin shugaban jam'iyyar All Blended Party (ABP)[1] na ƙasa kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a cikin ƴan takara 79 da suka fafata a zaɓen shugaban ƙasar Najeriya a shekarar 2019.[2][3][4][5][6]

Moses Shipi
Rayuwa
Haihuwa 1979 (44/45 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da ɗan kasuwa

Rayuwar farko gyara sashe

 
Moses Shipi

An haifi Moses Godia Shipi a ranar 2 ga watan Maris, 1979, a ƙauyen Boi, a ƙaramar hukumar Bogoro[7] dake Jihar Bauchi, Nijeriya. Mahaifinsa Musa Dawaki Shipi. Yayi karatunsa a makarantar firamare ta Boi Central, Bogoro LGA, Bauchi State da Gonerit Memorial College Tuwan Kabwir, Ƙaramar Hukumar Kanke ta Jihar Filato. Ya yi karatun digiri na farko a fannin Kiwon Lafiya a Jami'ar Abubakar Tafawa Ɓalewa.

Sana'a gyara sashe

Moses ya kasance ɗan jam'iyyar People's Democratic Party (PDP) a Najeriya. Daga shekarar 2007 zuwa 2010 ya kasance mataimaki na musamman ga Alh. (Dr) Malam Isa Yuguda kafin 2017 kafa jam'iyyar All Blended Party (ABP). Yana da shekaru 40 aka zaɓe shi a matsayin shugaban ABP na ƙasa wanda ya sanya shi zama mafi ƙarancin shekaru a cikin 91 da aka amince da shi a matsayin shugaban jam'iyyar siyasa ta ƙasa a Najeriya.[8][9][10] Ya kasance ɗan takarar shugaban ƙasa na All blended Party.

 
Shipi a taron Jam'iyya

Shi ne Babban Jami’in Gudanarwa (CEO) na La Shipson Construction Nigeria Limited, La Shipson Oil & Gas Nigeria Limited da La Shipson Shipping Company Nigeria Limited, la Shipson Hotel & Suits, la Shipson Travels and Tours, Moses Godia Shipi Foundation.[11][12][13]

Rayuwa ta sirri gyara sashe

Ya auri Angela Bulus Godia Shipi kuma suna da ƴaƴa biyu, Queenkyra Moses ship da King-Kendrick Moses ship.

Manazarta gyara sashe

  1. https://www.vanguardngr.com/2018/01/list-registered-political-parties-headquarters-addresses-principal-officers/
  2. https://www.xtra.net/news/politics/2019-list-presidential-candidates-political-parties-165978[permanent dead link]
  3. http://www.inecnigeria.org/?inecnews=registration-of-new-political-parties
  4. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-11-25. Retrieved 2023-03-15.
  5. https://dailypost.ng/2018/01/20/2019-election-full-list-registered-parties-addresses-principal-officers/
  6. https://theeagleonline.com.ng/moses-shipi-emerges-abp-presidential-candidate/
  7. https://www.mindat.org/feature-2346906.html
  8. https://pmnewsnigeria.com/2018/12/24/abp-dissolves-plateau-executive-council/
  9. https://theinterview.ng/2018/11/23/know-your-candidate-moses-shipi-abp/amp/
  10. https://punchng.com/number-of-political-parties-rises-to-91/
  11. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-05-06. Retrieved 2023-03-15.
  12. https://www.vanguardngr.com/2018/10/will-the-best-candidate-win/
  13. https://www.efccnigeria.org/efcc/news/2133-efcc-docks-man-for-n6-5m-fraud