Moses Kpakor
Moses Kpakor (an haife shi ranar 6 ga watan Janairun shekara ta alif ɗari tara da sittin da shida 1965A.c) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne mai ritaya wanda ya buga wa Najeriya wasa a gasar cin kofin Afirka ta shekarar 1990 a Aljeriya.
Moses Kpakor | |
---|---|
mutum | |
Bayanai | |
Jinsi | namiji |
Ƙasar asali | Najeriya |
Country for sport (en) | Najeriya |
Suna | Moses |
Shekarun haihuwa | 6 ga Janairu, 1965 |
Wurin haihuwa | Jahar Benue |
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa da association football manager (en) |
Matsayin daya buga/kware a ƙungiya | Mai buga tsakiya |
Mamba na ƙungiyar wasanni | Lobi Stars F.C. (en) , BCC Lions (en) , Abiola Babes (en) da Ƙungiyar ƙwallon ƙafar ta Najeriya |
Wasa | ƙwallon ƙafa |
Participant in (en) | 1990 African Cup of Nations (en) |
Sana'a
gyara sasheAn haife shi a jihar Benué, Kpakor ya fara buga wasan ƙwallon ƙafa a matsayin ɗan wasan tsakiya na tsaron gida na Hawks na Makurɗi. Zai buga gasar firimiya ta Najeriya tare da Electricity FC, BCC Lions FC da Abiola Babes a tsawon shekaru 18 yana aiki.[1] Ya lashe Kofin FA na Najeriya sau biyu (tare da Abiola Babes a cikin shekarar 1987 da BCC Lions a 1989) da kuma gasar cin kofin Afirka (tare da BCC Lions a shekara ta 1990).[2]
Kpakor ya buga wasanni da dama a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, ciki har da wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA a cikin shekarar 1994. Ya buga kowane wasa a gasar cin kofin nahiyar Afirka a cikin shekarar 1990, inda ya taimakawa Najeriya ta zama ta biyu.[3]
Bayan ya yi ritaya daga buga wasa, Kpakor ya zama kocin ƙwallon ƙafa. Ya jagoranci tsohon kulob ɗinsa, BCC Lions.
Na sirri
gyara sasheƊan Kpakor, Kelvin, shi ma ƙwararren ɗan ƙwallon ƙafa ne.[4]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Atoyebi, Olufemi (27 October 2012). "Police, EFCC should probe NPL over missing TV money –Moses Kpakor". Punch. Archived from the original on 27 October 2012. Retrieved 21 March 2014.
- ↑ Abu, Festus (11 May 2013). "'Westerhof saved Nigerian players' – Kpakor". Punch. Archived from the original on 10 January 2014. Retrieved 21 March 2014.
- ↑ Courtney, Barrie (12 June 2009). "African Nations Cup 1990 Final Tournament Details". RSSSF.
- ↑ "'I wanted to commit suicide', Say Moses Kpakor". Daily Sun. February 2011. Archived from the original on 2014-03-22. Retrieved 2023-04-17.
Hanyoyin haɗi na waje
gyara sashe- Moses Kpakor – FIFA competition record