Mohamed Baghlani (ya mutu a shekara ta 1977) ya kasance shugaban masu tayar da kayar baya na ƙasar Chadi a lokacin Yaƙin Basasar Chadi na Farko.

Mohamed Baghlani
Rayuwa
ƙasa Cadi
Mutuwa 1977
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Chadian National Union (en) Fassara

Sojojin Volcan sun fara fitowa a matsayin manyan rukuni ne a shekarar 1975. Shekarar da ta biyo bayan nan ne Ahmat Acyl ya shigo cikin kungiyar, sannan kuma a cikin watan Janairun shekarar 1977 tare da goyon bayan Libya suka hau sukar shugabancin Baghlani. Jim kaɗan bayan haka, a ranar 27 ga watan Maris, Baghlani ya kuma mutu tare da babban direbansa Mahamat Hissein a cikin wani hatsarin mota a Benghazi, a Libya wanda ake zargin hatsari ne daman da an rigaya aka shirya shi.