Moesha Buduong ƴar wasan kwaikwayo ce ta gidan talabijin Dan Ghana, 'yar wasan kwaikwayon kuma an san ta dalilin wata hira mai rikitarwa ga mai ba da rahoto na CNN Christiane Amanpour kan batutuwan jima'i, soyayya da jinsi.[1][2][3]

Moesha Buduong
Rayuwa
Haihuwa Kumasi, 10 ga Maris, 1990 (34 shekaru)
ƙasa Ghana
Mazauni Accra
Karatu
Makaranta University of Ghana
Accra Girls Senior High School
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a jarumi, model (en) Fassara da mai gabatarwa a talabijin
IMDb nm8197146

A watan Afrilu na shekara ta 2018, Buduong ta kasance ƙarƙashin zargi daga ƴan ƙasar Ghana. A kan wata hira mai rikitarwa da ta zanta a wani rahoto ga CNN Christiane Amanpour. A cikin hira, Buduong ta ambaci cewa matan Ghana suna amfani da maza a matsayin tushen samun kuɗin shiga, tunda tattalin arziki yana da wahala. Suna yin hakan ta hanyar yin jima'i da maza. [4] An nakalto ta tana cewa "A Ghana, tattalin arzikinmu hanya ce da kuna buƙatar wani don kula da ku. Ba za ku iya samun isasshen kuɗi a matsayin mace a nan ba. Saboda ko da lokacin da kuke son samun gida, a Ghana suna ɗaukar shekaru biyu" ci gaba kuma na fara aiki inda zan sami kuɗi don biyan?" Maganganunta ta sami zargi mai tsanani daga maza da mata waɗanda suka ji tana batama Ghana suna (da kuma ta Afirka). Mutane kamar John Dumelo, Lydia Forson, Eazzy, DKB da Afia Odo sun bayyana ra'ayoyinsu a kan Twitter, mafi yawan ra'ayoyin na suka ne.

Manazarta

gyara sashe
  1. "Watch Moesha Boduong's complete interview with CNN's Amanpour". Graphic Online (in Turanci). 2018-04-24. Retrieved 2019-03-09.
  2. "Don't condemn Moesha Boduong – CNN's Amanpour". www.ghanaweb.com (in Turanci). Retrieved 2019-03-09.
  3. Ofori-Boateng, Pamela. "A CNN interview sparked another Ghana backlash and a debate about women, sex and love". Quartz Africa (in Turanci). Retrieved 2019-03-09.
  4. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named :0

Hanyoyin Hadi na waje

gyara sashe