Miyar zogale

Miyar zogale abinci ne na hausa wanda aka fi sani da miya .Ana yin shi da ganyen zogale a matsayin babban sinadari, wannan miyar tana da dadi kuma cinsa magani ne yana kara lfy a jikin mutun.

Miyar zogale yana da kyau tare da biskin masara, alkama, semovita, dawa da tuwo shinkafa.[1]

Yadda ake miyar zogale

  • Tattasai
  • Attarugu
  • Albasa
  • Zogale
  • Maggie
  • Gishiri
  • Garlic thyme
  • Seasoning spices
  • Nama
  • Kifi busashshe
  • Man ja or man gyada
  • Gyada

YADDA ZA’A HADA MIYAR ZOGALE gyara sashe

Da fari zaki tafasa nama ki sanya thyme da maggie da albasa bayan ya tafasa saiki sanya mai a tukunya ki soyashi da albasa saiki zuba kayan miyarki ki kuma sanya naman da kika tafasa tare da ruwan da kika tafasa naman.[2]

Saiki zuba gyadar ki wadda kin riga kin gyarata kin daka ta da busashshen kifin ki shima bayan ki gyara abunki saiki sanya curry da maggie gishiri saiki barshi yayi kamar mintuna goma (10) saiki zuba zogalen ki bayan kin gyarashi.[3]

Anaso ki zuba zogalen da yawa domin anfiso miyar tayi kauri saiki barshi kan wuta yayi a kalla kamar mintuna sha biyar (15) shikenan saiki sauke. Miyarki yayi dai dai kuma a shirye yake wajen ci.

Manazarta gyara sashe

  1. "Miyan Zogale (Moringa soup)". Vanguard News. 2017-06-06. Retrieved 2022-06-20.
  2. "Hausa Foods | How To Make Nigerian Foods". All Nigerian Foods. Retrieved 2022-06-20.
  3. "NIGERIAN LOCAL DISH: MIYAN ZOGALE (MORINGA SOUP)". EveryEvery. 2019-04-07. Retrieved 2022-06-20.