Miyar Ogbono

Miyar Najeriya mai arziki da aka yi da busasshen ƙasa irvingia tsaba (Ogbono seed). Ana iya cin sa da fufu ko doyar dawa.

Miyar Ogbono, miya ce da ake ci a Najeriya wacce ake yinta da niƙaƙƙen busasshen tsabar ogbono. Ana samun irin Ogbono a Kudancin Najeriya kuma a can aka fara shuka ta.[1][2][3] (ana kiran sa da Irvingia a gargajiyance)[4][5] kuma tana da iri daban daban. Dangane da bincike da Chris Chinaka da J.C. Obiefuna suka yi sun nuna cewa Ogbono bishiyar gandun daji ce ta asali da ke hade da tsirrai da aka ware su a matsayin 'kayan dajin da ba na itace ba. Ana kiransa da sunaye daban-daban a Najeriya. A yankin da ake magana da harshen Ibo ana kiransa 'ogbono/ugiri' ya danganta da nau'in Ibo. A Nupe, ana kiransa 'pekpeara', 'ogwi' a harshen Bini, 'uyo' a harshen Efik sannan kuma ana kiransa 'oro' a da Yarbanci.[6]

Miyar Ogbono
miya
Kayan haɗi dika nut (en) Fassara, palm oil (en) Fassara, stockfish (en) Fassara, naman shanu, salt (en) Fassara, ruwa, albasa, seasoning (en) Fassara da spinach (en) Fassara
Tarihi
Asali Najeriya

Ana amfani da 'ya'yan ogbono don ƙara wa miya kauri da kuma sanya mata baƙin launi.[4] Bayan tsaba, ruwa da manja, yawanci ana sanya wa miyan nama da kayan yaji kamar barkono,[4] kayan ganye da makamantansu. Ganyayyakin ganye na yau da kullun sun haɗa da bitterleaf da celosia. Sauran kayan ganye na yau da kullun sun haɗa da tumatir da okra. Kayan yaji sun haɗa da borkono, albasa, da iru (wake).[4] Nama kuwa sun haɗa da naman sa, na akuya, kifi,[4] kaza, naman daji, jawa, ko crayfish.

Ana iya cin shi da fufu,[4] ko kuma da sakwara. A wasu ƙasashen ana iya samun miyan a gyare a wasu kasuwannin da suka kware kan abinci irin na yammacin Afirka.[4] Miyar Ogbono tana da yauƙi,[7] mai kama da miyar kuɓewa.

Manazarta gyara sashe

  1. Atiku, M.K. (2003). Strengthening Food and Beverages Quality Standards and Safety as a Stimulant for Industrial Growth. Nigerian Institute of Food Science and Technology. p. 178. Retrieved October 2, 2018.
  2. "Ogbono Soup". Tribune Online (in Turanci). 2018-12-01. Retrieved 2022-05-11.
  3. "Ogbono - UdyFoods" (in Turanci). Retrieved 2022-05-11.
  4. 4.0 4.1 4.2 4.3 4.4 4.5 4.6 Wright, Clifford A. (2011). The Best Soups in the World. John Wiley & Sons. p. 51. ISBN 978-1118109250.
  5. "IRVINGIA GABONENSIS: Overview, Uses, Side Effects, Precautions, Interactions, Dosing and Reviews". www.webmd.com (in Turanci). Retrieved 2022-05-11.
  6. Edozie, V (2016). "Ogbono trees vanishing in Bayelsa". Daily Trust.
  7. Odumade, Omotolani (May 21, 2018). "Soups every Nigerian should be able to make". Pulse.ng. Retrieved October 2, 2018.