Marie-Angélique Savané (née Sagna, an haife ta biyu 2 ga watan Nuwamba 1947) ƙwararriyar ilimin zamantakewa ce kuma mai fafutuka akan mata, wacce ta kasance "mai matuƙar goyon bayan gyare-gyaren doka da zamantakewa a cikin al'ummar Senegal a madadin mata", a cewar ƙamus na Tarihin Afirka. . An kira ta daya daga cikin jagaban matan Afirka.

Rayuwar farko gyara sashe

An haife ta a ranar biyu 2 ga watan Nuwamba a shekara ta 1947 a Dakar, Senegal, cikin dangin Katolika .

Sana'arta gyara sashe

Daga 1974 zuwa 1978, Savané ta kasance Babbar Editan Mujallar Famille et Développement (Family and Development), "mujallar taimakon kai da kai a yankin Saharar Afrika". A lokacin da take rike da mukaminta ta mayar da mujallar daga yammacin Afirka zuwa wani ra'ayi na Afirka, akan "taimakawa 'yan Afirka su taimaki kansu". [1]

Savané ta yi aiki ga Majalisar Dinkin Duniya, kuma a matsayin mai ba da shawara ga kungiyoyin Majalisar Dinkin Duniya daban-daban na tsawon shekaru masu yawa.

Savané mai haɗin gwiwa ce ta Ƙungiyar Matan Afirka don Bincike.

Rayuwarta ta sirri gyara sashe

Ta yi aure da Landing Savane Wanda (an haife shine a shekara ta 1945) ɗan siyasan Senegal na hagu, kuma Sakatare-Janar na And-Jëf / Jam'iyyar Afirka ta Dimokuradiyya da Socialism .

Su ne iyayen ga ƙwararren ɗan wasan ƙwallon kwando Sitapha Savané .

Nassoshi gyara sashe

  1. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named auto1