Mamayewar Rasha a Ukraine na 2022
A ranar 24 ga Fabrairun shekarar 2022, Rasha ta ƙaddamar da wani gagarumin farmaki a Ukraine, maƙwabciyarta ta kudu maso yammacin ƙasar, wanda hakan ke nuna ruruwar cigaban yaƙin dake gudana tsakanin Rasha da Ukraine tun daga shekara ta 2014. Sakamakon ƴanci da Ukraine ta samu na zama da kanta a shekarar 2014, wannan yaƙin an ayyana shi a matsayin mafi girman tashin hankali da ba'a taɓa gani ba a turai tun bayan yaƙin duniya. Akan kalli sanadin amatsayin Rasha tana son haramtawa Ukraine shiga ƙungiyar NATO bisa doka,[1] ƙawancen ƙasashen Turai tare da Amurka da Kanada. Kafin kai farmakin sai da Rasha ta amince da wasu jihohin Ukraine guda biyu da suka ayyana kansu amatsayin yan tattun ƙasashe, wato Jamhuriyar Jama'ar Donetsk da Jamhuriyar Jama'ar Luhansk, sannan kuma sojojin Rasha suka fara mamaye yankin Donbas na gabashin Ukraine a ranar 21 ga watan Fabrairun shekarar 2022.
Da misalin ƙarfe 03:00 UTC (06:00 Moscow Time, MSK) a ranar 24 ga Fabrairu, shugaban Rasha Vladimir Putin ya bada sanarwar wani farmakin soji a gabashin Ukraine; mintuna kaɗan bayan haka, aka fara kai hare-haren manyan makamai a wurare daban-daban a cikin biranen ƙasar musamman ma wajajen jami'an tsaron ƙasar, ciki har da babban birnin ƙasar Kyiv da ke arewacin ƙasar. Hukumar kula da kan iyakokin ƙasar Ukraine ta bayyana cewa an kai wa kan iyakokinta da Rasha da Belarus hari.[2][3] Bayan sa'o'i biyu, sojojin kasa sun shiga da misalin karfe 05:00 UTC.[1] Ƙasashe da dama sun yi tir da harin tare da sanyawa Rasha takunkumi.[4]
Hotuna
gyara sashe-
Sojojin Eukraniya kafin fara gwabza yaƙin
-
Sign Lviv Volunteer Centre.
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 "Why is Russia invading Ukraine and what does Putin want?". BBC News (in Turanci). 24 February 2022. Archived from the original on 19 December 2021. Retrieved 24 February 2022.
- ↑ "Russia attacks Ukraine". CNN. 24 February 2022. Archived from the original on 24 February 2022. Retrieved 24 February 2022.
- ↑ "Украинские пограничники сообщили об атаке границы со стороны России и Белоруссии". Interfax. 24 February 2022. Archived from the original on 24 February 2022. Retrieved 24 February 2022.
- ↑ Morin, Rebecca (24 February 2022). "World leaders condemn Russian invasion of Ukraine; EU promises 'harshest' sanctions – live updates". USA Today. Archived from the original on 24 February 2022. Retrieved 24 February 2022.