Mahmood Ali-Balogun dan fim ne dan Najeriya, ma'aikacin al'adu kuma Manajan darakta na Kamfanin Brickwall Communications Limited. Ya shirya fim din da ya lashe kyauta mai yawa 'Tango Tare Ni'. Shi ne Shugaban kungiyar Audio Visual Rights Society (AVRS) a Nigeria.

Mahmood Ali-Balogun
Rayuwa
Haihuwa 19 ga Yuli, 1959 (65 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƴan uwa
Abokiyar zama Nkechi (en) Fassara
Karatu
Makaranta Jami'ar Obafemi Awolowo
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a darakta, marubuci da cultural worker (en) Fassara
Muhimman ayyuka Tango With Me
Kyaututtuka
Imani
Addini Musulunci
IMDb nm3123654

Rayuwa da aiki

gyara sashe

An haifi Mahmood Ali-Balogun a ranar 19 ga watan Yulin 1959 [5] kuma ya girma a Arewacin Najeriya. Shi tsofon dalibin Jami’ar Ife ne, yanzu kuma Jami’ar Obafemi Awolowo ce inda ya karanci Dramatic Arts kuma ya kware a harkar fim da talabijin. Ayyukan Mahmood sun samo asali tsawon shekaru daga kasancewa ɗan wasa, zuwa darekta, furodusa, shugaban masana'antu, mai ba da shawara kan fim da kuma jakada a cikin masana'antar yin Fina-finai. http://www.ama-awards.com/mahmood-ali-balogun Archived 2014-03-13 at the Wayback Machine