Lola Ade-John kwararriyar bayanai da fasaha ce ta Najeriya, ma'aikaciyar banki kuma ministar yawon bude ido a yanzu.[1]

Lola Ade-John
Minister of Tourism (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa jahar Legas
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Ibadan
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Yarbanci
Sana'a
Sana'a civil servant (en) Fassara da Ma'aikacin banki
Employers Shell Nigeria
Ecobank Nigeria (en) Fassara
Bankin Access
United Bank for Africa
Imani
Addini Kirista
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress

Lola Ade-John ta yi karatun kimiyyar kwamfuta a jami'ar Ibadan inda ta kammala a shekarar 1984. Ta kuma yi digiri na biyu a fanni daya da jami’a guda.[1]

Bayan kammala karatunta daga jami'a, Lola ta yi aiki tare da Shell Petroleum a matsayin manazarcin tsarin. Sannan ta ci gaba da aiki da bankin Magnum Trust, Bankin Access, Bankin United Bank for Africa da Ecobank . Bayan aikinta a fannin banki, ta kafa Novateur Business Tecchnology Consultants a cikin 2013.

A ranar 16 ga Agusta 2023, Shugaba Bola Tinubu ya nada ta ministar yawon bude ido. Ta hau ofis a ranar 21 ga Agusta 2023.[2][3]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 Ekugo, Ngozi (2023-08-03). "Meet Lola Ade-John, IT and banking expert on the ministerial nomination list". Nairametrics (in Turanci). Retrieved 2023-08-21.
  2. Aworinde, Oluwatobi (16 August 2023). "Full List: Portfolios Of Tinubu's 45 Ministers". Channels TV. Retrieved 21 August 2023.
  3. "Tour operators: How Lola Ade-John can succeed as tourism minister - P.M. News" (in Turanci). Retrieved 2023-08-21.