KWANKWASIYYA Wani bangaren Siyasa ne a Najeriya wanda Sanata Rabiu Kwankwaso ya kafa. Farko dai Kwankwasiyya ta fara ne a jihar Kano kafin daga bisani kuma akidar ta yadu ko ina cikin fadin kasar Najeriya.

Kwankwasiyya
gadan kwankwasiyya

Tsarin tafiyar Kwankwasiyya ya ginu ne akan akida da jajircewa da kuma duk abinda yayanta suka saka a gaba, an san yan Kwankwasiyya da nacin tsiya, basa tsoron tunkarar gwamnati da adawa, kuma sun kware wajen adawa domin duk wanda suka sako a gaba da wuya kaga yasha, su suka yi sanadiyar kifar da gwamnatin malam Ibrahim shekarau a jihar Kano a 2011, sannan sun taimaka wajen kifar da gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan a shekarar 2015.

A tsarin [[Kwankwasiyya ba'a bayar da kudi domin mutum yazo taro, a mafi yawancin tarurrukansu duk wanda ka gani shi ya kai kansa, kuma tunda suka kafa gwamnati a jihar Kano a shekarar 2011, suka kawo sabon tsarin siyasa na fita kamfen ba tare da daukar makamai ba, koni burina nazama kamar kwankwaso akasata Nigeria burina ace ko wacce state ace takasance kamar KANO da JIGAWA inshallah sai nazama kamar Mai gida kwankwaso a Nigerian buri ko Ina agyara nine Saminu B madaki masoyin kwankwasiya Amana.

Tarihin Kwankwasiyya.

gyara sashe

Kwankwasiyya PDP

gyara sashe

Asalin jam'iyyar da Sanata Kwankwaso jagoran Kwankwasiyya yake kuma yaci zabubbukan gwamna a shekarar 1999, da 2011, itace jam'iyyar PDP. Sakamakon rikicin cikin gida a lokacin da bangaren PDP na Marigayi Abubakar Rimi ne Kwankwaso ya kafa akidar sa ko kungiyar Kwankwasiyya a jahar Kano. Haka tsagin yayi ta samun tagomashi har zuwa lokacin da jagoran PDP kwankwasiyya Sanata Rabiu Kwankwaso ya canza sheka daga ja'iyyar PDP zuwa ta APC.

Kwankwasiyya APC.

gyara sashe

Tun bayan da Sanata Rabiu Kwankwaso ya canza sheka daga jam'iyyar PDP zuwa sabuwar jam'iyyar APC ne sauran magoya bayan sa suma suka bishi zuwa jam'iyyar ta APC tare da kafa akidar ta Kwankwasiyya a jihar kano. A zabubbukan da suka gudana a shekarar 2015, ne akidar ta kwankwasiyya ta yadu ko ina cikin fadin kasar sakamakon tsayawar takarar shugabancin kasar da Sanata kwankwaso yayi wanda yayi rashin nasara a hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayin zaben fidda gwani na jam'iyar APC.

Kwankwasiyya PDP a karo na biyu.

gyara sashe

Bayan Buhari ya lashe zaɓe a 2015, jagoran Kwankwasiyya ya zarge shi da rashin basu muhimmanci inda ya hana su muƙaman gwamnati kamar yadda aka saba idan ka taimaka an kafa gwamnati, sannan Kwankwaso yayi zargin shugaba Buhari baya ɗaukar shawara, daga bisani dai a shekarar 2018, jagoran Kwankwasiyya Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar APC zuwa PDP, kuma nan take magoya bayansa suka rufa masa baya da shan alwashin kayar da jam'iyyar APC a zaɓukan 2019, tun daga sama har ƙasa.