Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Hussaini Adamu

Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Hussaini Adamu ko (Hussaini Adamu Federal Polytechnic (HAFEDPOLY) tana a Garmin Kazaure, Jihar Jigawa, Najeriya . An kirkiro ta ne a watan Disambar 1991 a matsayin Kwalejin Fasaha ta Jihar Jigawa, tare da kwalejoji huɗu a wurare daban-daban. Wadannan sune Kwalejin Injiniya, Kimiyya da Fasaha a Kazaure, Kwalejin Kasuwanci da Nazarin Gudanarwa a Dutse, Kwalejin Addinin Musulunci da Shari'a a Ringim da Kwalejin Aikin Gona a Hadejia . Har ila yau, Cibiyar ta Tsakiya tana Kazaure. Manufar kwalejin ita ce "samar da horo kan fasaha da dabarun aiki domin biyan bukatun ma'aikata na ci gaban Masana'antu da Tattalin Arzikin Najeriya."

Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Hussaini Adamu
Bayanai
Iri polytechnic (en) Fassara
Ƙasa Najeriya
Harshen amfani Turanci
Tarihi
Ƙirƙira 1991
hafedpoly.edu.ng

An sauya wa kwalejin suna Hussaini Adamu Polytechnic a 1998, don girmama tsohon sarkin Kazaure, Alhaji Hussaini Adamu. Ya zama kwalejin kimiyya ta tarayya a cikin Janairu 2007. A watan Fabrairun 2009, cibiyar ta gudanar da taronta na farko, inda ta ba da takardar sheda da difloma ta kasa ga dalibai 6,024 da suka kammala karatu tsakanin 1992 da 2008.

Ɗakin karatu

gyara sashe

An gina katafariyar dakin karatun ne a shekarar 2009, a karkashin shirin bayar da tallafi na Asusun Ilimi na shekara ta 2009. An tsara shi da kyau don saduwa da mafi kyawun aikin duniya.

Laburaren ya kunshi e-laburare (wato na yanar gizo) da babban laburare, babban dakin karatu yana dauke da littattafai ga duka malamai da dalibai. Akwai ɗakunan ajiya sama da goma a cikin babban ɗakin karatu.

E-laburaren wani sabon yanki ne na tsarin fasahar isar da sako na zamani, kuma shaidar ci gaba ne a fannin fasahar sadarwa a Najeriya . E-laburaren yana da haɗin hanyar sadarwa mara waya kuma an haɗa shi da dukkan kwamfutocin da ke cikin e-library kuma ana amfani da shi don dalilai na ilimi kawai.

Duba Kumaa

gyara sashe
  • Jerin ilimin fasaha a Najeriya

Manazarta

gyara sashe