Kwabena Donkor
Kwabena Donkor (an haife shi 5 ga watan Fabrairu 1958) ɗan siyasan Ghana ne kuma tsohon Ministan wutar lantarki.[1] Shi ne dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Pru ta gabas, a yankin Bono ta Gabas ta Ghana.[2] Ya yi murabus daga mukaminsa na minista ne sakamakon gaza kawo karshen dimbin lodin da ake yi wa lakabi da Dumsor, inda ya yi alkawarin yin murabus idan har bai warware wannan batu ba kafin karshen shekarar 2015.[3][4]
Kwabena Donkor | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|
7 ga Janairu, 2021 - District: Pru East Constituency (en) Election: 2020 Ghanaian general election (en)
7 ga Janairu, 2017 - District: Pru East Constituency (en) Election: 2016 Ghanaian general election (en)
7 ga Janairu, 2013 - 6 ga Janairu, 2017 District: Pru East Constituency (en) Election: 2012 Ghanaian general election (en) | |||||||
Rayuwa | |||||||
Haihuwa | Lonto, 5 ga Faburairu, 1958 (66 shekaru) | ||||||
ƙasa | Ghana | ||||||
Karatu | |||||||
Makaranta |
University of Leicester (en) MBA (mul) : strategic management (en) University of Bristol (en) Doctor of Philosophy (en) : Development Management (en) , industrial relations (en) University of Bristol (en) Master of Science (en) | ||||||
Harsuna | Turanci | ||||||
Sana'a | |||||||
Sana'a | ɗan siyasa da consultant (en) | ||||||
Wurin aiki | Accra | ||||||
Imani | |||||||
Addini | Kirista | ||||||
Jam'iyar siyasa | National Democratic Congress (en) |
Shekarun farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Donkor a ranar 5 ga Fabrairu, 1958, a Lonto ta hanyar Yeji a yankin Bono Gabas ta Ghana. Ya yi digirin digirgir (PhD) da na biyu a jami'ar Bristol, sannan kuma ya yi digiri na biyu a fannin harkokin kasuwanci daga jami'ar Lancaster.[1]
Aiki
gyara sasheDonkor ya kasance mataimakin ministan yada labarai daga 2013 zuwa 2014. Mamba ne wanda ya kafa hukumar kula da albarkatun man fetur kuma ya kasance babban jami’in hukumar a shekarar 2014. A wannan shekarar ya zama minista a gwamnatin Ghana. Ya zama dan majalisar dokokin Ghana a shekarar 2015 kuma ya zama shugaban kwamitin ma'adinai da makamashi.[1][5] A halin yanzu yana wakiltar mazabar Pru ta gabas a yankin Bono ta gabas a kan tikitin jam'iyyar National Democratic Congress.[1][6]
Siyasa
gyara sasheDonkor ya tsaya takarar kujerar dan majalisar wakilai ta Pru East a zaben 2016 kuma ya yi nasara. Ya samu kuri'u 13,512 wanda ke wakiltar kashi 56.19% na yawan kuri'un da aka kada, don haka ya doke sauran 'yan takarar da suka hada da David Amoah, Danjumah Desmond, Noah Ken Boadai da Zevor Mattew Tsiditsey.[7] Ya ci gaba da rike kujerarsa a babban zaben Ghana na 2020.[8]
Kwamitoci
gyara sasheDonkor shi ne Mamba mai Daraja a Kwamitin Samar da Aiki, Jin Dadin Jama'a da Kamfanonin Jiha; kuma memba na Kwamitin Tsare-tsare na oda; sannan kuma memba na kwamitin ma'adinai da makamashi.[9]
Rayuwa ta sirri
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 1.3 "Hon. Kwabena Donkor (Dr)". parliament.gh. Archived from the original on 6 August 2016. Retrieved 30 December 2015.
- ↑ "ACEP urges Kwabena Donkor to admit failure and resign". Myjoyonline.com. 26 December 2015. Retrieved 30 December 2015.
- ↑ Darfah Frimpong, Enoch (31 December 2015). "Confirmed: Kwabena Donkor resigns over dumsor controversy". graphic.com.gh. Retrieved 1 January 2016.
- ↑ "Power Minister resigns over Dumsor". citifmonline.com. 31 December 2015. Archived from the original on 2 January 2016. Retrieved 1 January 2016.
- ↑ "Celebrating The Man Dr. Kwabena Donkor (Pt.1)". Modern Ghana (in Turanci). Retrieved 2020-01-31.
- ↑ "Dr Kwabena Donkor | Annual Ghana Summit". www.cwcghana.com. Archived from the original on 2020-01-31. Retrieved 2020-01-31.
- ↑ FM, Peace. "Ghana Election 2016 Results – Pru East Constituency". Ghana Elections – Peace FM. Archived from the original on 2020-01-31. Retrieved 2020-01-31.
- ↑ "Parliamentary Results for Pru East". www.ghanaweb.com. Retrieved 11 January 2021.
- ↑ "Parliament of Ghana". www.parliament.gh. Retrieved 2022-11-18.
- ↑ "Ghana MPs – MP Details – Donkor, Kwabena (Dr)". www.ghanamps.com. Retrieved 2020-01-31.
- ↑ "Ghana Parliament member Kwabena Donkor (Dr)". www.ghanaweb.com. Retrieved 2020-01-31.[permanent dead link]