Koutoub Moustapha Sano (an haife shi a ranar 10 ga watan Afrilu, 1966) ɗan siyasa ne kuma malami daga Guinea. Ya taɓa rike muƙamin ministan ofishin shugaban ƙasar Guinea kuma mai baiwa shugaban ƙasar shawara kan harkokin diflomasiyya. Yana da digirin digirgir a fannin shari'a.[1] [2][3]

Koutoub Moustapha Sano
minister-counselor (en) Fassara

18 ga Maris, 2016 -
Minister of African Cooperation and Integration (en) Fassara

2011 - 2016
Secretary General of Religious Affairs of Guinea (en) Fassara

2009 - 2010
Rayuwa
Haihuwa Kankan (en) Fassara, 10 ga Afirilu, 1966 (58 shekaru)
ƙasa Gine
Karatu
Makaranta King Saud University (en) Fassara licentiate (en) Fassara : comparative law (en) Fassara
International Islamic University Malaysia (en) Fassara DES (en) Fassara : banki, financial economics (en) Fassara
International Islamic University Malaysia (en) Fassara Doctor of Philosophy (en) Fassara : comparative law (en) Fassara
King Saud University (en) Fassara master's degree (en) Fassara : comparative law (en) Fassara
Ez-Zitouna University (en) Fassara doctorate in France (en) Fassara : Sharia-compliant banking (en) Fassara
Harsuna Faransanci
Larabci
N'Ko harshe
Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Addini Musulunci

Tarihin Rayuwa

gyara sashe

An haife shi a Kankan, Guinea, ɗa ne ga Elhadj Sidafa Sano da Hadja Aissata Koma.[4]

 
Taron IIFA na 3 a Madina (Saudi Arabia) a cikin 2018
  • A cikin shekarar 1989 ya sami digiri mai zurfi a cikin harshen Faransanci daga Ma'aikatar Ilimi ta Jamhuriyar Faransa.
  • Digiri na farko a fannin ilimi (Comparative Law) a shekarar 1990, sannan ya yi digiri na biyu a fannin shari'a tare da (distinction) a Jami'ar King Saud a shekara ta 1993.[5]
  • Doctorate a cikin falsafar shari'a a Jami'ar International ta Malaysia a shekarar 1996
  • Ya samu digirin digirgir a fannin banki da harkokin kuɗi na Musulunci a Jami'ar Musulunci ta ƙasa da ƙasa Malaysia a shekarar 1998.
  • A shekara ta 2001, ya sami digiri na uku a fannin kuɗi na Musulunci tare da karramawa daga Jami'ar Zaitouna da ke Tunisiya.

Girmamawa da kyaututtuka

gyara sashe
 
Koutoub Moustapha Sano
  • Kyautar Mafi kyawun ɗalibi na Jami'ar King Saud a Riyadh a shekara ta 1989.
  • Ya samu lambobin zinare 25 a gasar jami'o'i daban-daban a ƙasar Saudiyya.
  • Kyautar The Favorite Personality na Guinean na shekarun 2012-2013.
  • Kyautar Mafi kyawun Ministan Jamhuriyar Gini 2012-2015.

Yayin da yake mataimakin rector (2005-2009) mai kula da harkokin ƙasa da ƙasa da kirkire-kirkire a Jami'ar Musulunci ta ƙasa da ƙasa Malaysia, tsohon Sultan na Pahang, yanzu Sarkin Malaysia (2019-), ya ba shi lambar girma ta Dato a shekara ta 2007.[6]

A watan Oktoban 2020, ya karɓi muƙamin babban sakatare na Kwalejin Fiqh ta ƙasa da ƙasa bayan ya rike muƙamai na tsawon shekaru goma sha biyu a Kwalejin Shari'a da ke Jeddah. Daga shekarun 1993 zuwa 2009, ya kasance farfesa a fannin shari'a da kuma harkokin kuɗi na Musulunci a IIUM. Daga shekarun shekara ta 2005 zuwa 2009 ya zama mataimakin shugaban jami'ar Musulunci ta ƙasa da ƙasa Malaysia. Ya taɓa rike muƙamin ministan harkokin addini na kasar Guinea daga shekarun 2009 zuwa 2010, ministan haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa da haɗin gwiwar ƙasashen Afirka daga shekarun 2011 zuwa 2016,[7] shugaban majalisar ministocin kungiyar kogin Mano daga shekarun 2014 zuwa 2015. [8] An naɗa shi a matsayin mai ba wa shugaban ƙasar Guinea shawara kan harkokin diflomasiyya daga ranar 18 ga watan Maris, 2016, zuwa yanzu.

Manazarta

gyara sashe
  1. "Pr Koutoubou Moustapha SANO : " La violence et la division doivent cesser en Guinée… "" (in Faransanci). 22 February 2018. Archived from the original on 7 July 2022. Retrieved 10 December 2023.
  2. "Rénovation de la Mosquée Fayçal : Dr Koutoubou Sano accuse". Aminata ! actualité de la Guinée. 16 July 2017.
  3. "Koutoubou Sano : " le CNDD, la transition et moi… "". Africaguinee.com - Site officiel d'informations sur la Guinée et l'Afrique (in Faransanci). 2017-09-30. Archived from the original on 2018-07-04. Retrieved 2018-07-04.
  4. "Nécrologie : décès en Belgique de Hadja Aïssata Koma, mère du ministre Koutoubou Sano" (in Faransanci). Mosaiqueguinee.com. Archived from the original on 2018-03-31. Retrieved 2018-07-04.
  5. "Nécrologie : décès en Belgique de Hadja Aïssata Koma, mère du ministre Koutoubou Sano" (in Faransanci). Mosaiqueguinee.com. Archived from the original on 2018-03-31. Retrieved 2018-07-04.
  6. "Advisor to President of Guinea joins Muslim Council of Elders".
  7. "Pr Koutoubou Moustapha SANO : «La violence et la division doivent cesser en Guinée… »". Archived from the original on 2022-07-07. Retrieved 2023-12-10.
  8. "Pr Koutoubou Moustapha SANO : «La violence et la division doivent cesser en Guinée… »". Archived from the original on 2022-07-07. Retrieved 2023-12-10.