Kofi Frimpong (an haife shi a ranar 17 ga watan Yuni 1951) [1] [2] ɗan kasuwa ne [1] [2] kuma ɗan siyasar Ghana na Jamhuriyar Ghana. [1] Ya kasance dan majalisa mai wakiltar mazabar Kwabre ta gabas na yankin Ashanti na Ghana a majalisa ta 4 da 5 da ta 6 a jamhuriya ta hudu ta Ghana. [3] [4] [5] [6] [7] Dan sabuwar jam'iyyar kishin kasa ne . [2] [1] [8][9] [10]

Kofi Frimpong
Member of the 6th Parliament of the 4th Republic of Ghana (en) Fassara

7 ga Janairu, 2013 - 6 ga Janairu, 2017
District: Kwabre East Constituency (en) Fassara
Election: 2012 Ghanaian general election (en) Fassara
Member of the 5th Parliament of the 4th Republic of Ghana (en) Fassara

7 ga Janairu, 2009 - 6 ga Janairu, 2013
District: Kwabre East Constituency (en) Fassara
Election: 2008 Ghanaian general election (en) Fassara
Member of the 4th Parliament of the 4th Republic of Ghana (en) Fassara

7 ga Janairu, 2005 - 6 ga Janairu, 2009
District: Kwabre East Constituency (en) Fassara
Election: 2004 Ghanaian general election (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Ntonso (en) Fassara, 17 ga Yuni, 1951 (73 shekaru)
Karatu
Makaranta University of Ghana Bachelor of Arts (en) Fassara : kimiyar al'umma
Sana'a
Sana'a ɗan kasuwa da ɗan siyasa
Imani
Addini Kiristanci

Ƙuruciya da ilimi

gyara sashe

An haifi Frimpong a ranar 17 ga Yuni 1951. [11] Ya fito daga Ntonso, wani gari a yankin Ashanti na Ghana. [1] [2] Ya fito ne daga Jami'ar Ghana (UG). [1] [2] Ya yi digirin digirgir a fannin zamantakewa da kimiyyar siyasa daga jami'a. [1] [2] Ya sami digiri a shekarar 1978. [1] [2]

Frimpong ɗan kasuwa ne. Ya kasance manajan darakta na Bakota Medical Technology Limited a Kumasi. [1] [2] Wannan shi ne kafin ya tsaya takarar siyasa a shekarar 2004. [1] [2]

Sana'ar siyasa

gyara sashe

Frimpong memba ne na Sabuwar Jam'iyyar Patriotic. Ya zama dan majalisa daga watan Janairun 2005 bayan ya yi nasarar lashe zabe a watan Disamba na shekarar 2004. Ya sake tsayawa takara karo na biyu kuma ya yi nasara. [3] [4] [12] Ya kasance dan majalisa mai wakiltar mazabar Kwabre East. [2] [1] An zabe shi a matsayin dan majalisa na wannan mazaba a majalisa ta hudu da ta biyar da ta shida a jamhuriyar Ghana ta hudu. [12] [7] [6] [5] [4] [3] [2] [1]

An zabi Frimpong a matsayin dan majalisa mai wakiltar mazabar Kwabre ta gabas na yankin Ashanti na kasar Ghana a karon farko a babban zaben Ghana na shekara ta 2004. Ya yi nasara akan tikitin sabuwar jam'iyyar Patriotic Party. [3] [4] Mazabarsa wani bangare ne na kujeru 36 na 'yan majalisa daga cikin kujeru 39 da sabuwar jam'iyyar Patriotic Party ta lashe a wancan zaben na yankin Ashanti.[13] Sabuwar jam'iyyar Patriotic Party ta samu rinjayen kujeru 128 na 'yan majalisa daga cikin kujeru 230.[14] An zabe shi da kuri'u 42,094 daga cikin 51,871 da aka kada. [3] [4] Wannan yayi daidai da kashi 81.2% na jimlar ƙuri'un da aka jefa. [3] [4] An zabe shi a kan Augustine Yeboah Domfeh na National Democratic Congress da Agnes Donkor na Jam'iyyar Convention People's Party . [3] [4] Wadannan sun samu kuri'u 8,906 da 871 bi da bi na yawan kuri'un da aka kada. [3] [4] Waɗannan sun yi daidai da 17.2% da 1.7% bi da bi na jimlar ingantattun ƙuri'un da aka jefa. [3] [4]

A shekarar 2008, ya lashe zaben gama gari a kan tikitin sabuwar jam'iyyar Patriotic Party na wannan mazaba. Mazabarsa tana cikin kujeru 34 na 'yan majalisa daga cikin kujeru 39 da sabuwar jam'iyyar Patriotic Party ta lashe a wancan zaben na yankin Ashanti.[15] Sabuwar jam'iyyar Patriotic Party ta lashe kujerun 'yan majalisa 109 daga cikin kujeru 230.[16] An zabe shi da kuri'u 41,454 daga cikin 54,517 da aka kada. [5] [6] Wannan yayi daidai da 76.04% na jimlar ingantattun ƙuri'un da aka jefa. [6] [5] An zabe shi a kan Bismark Adu-Asere na National Democratic Congress, Zacharia Awuah na Democratic Freedom Party da Alice Duah Boateng na Convention People's Party . [5] [6] Wadannan sun samu kuri'u 10,824, 555 da 1,684 bi da bi na yawan kuri'un da aka kada. [5] [6] Wadannan sun yi daidai da 19.85%, 1.02% da 3.09% na jimillar kuri'un da aka kada. [6] [5]

A shekarar 2012, ya sake lashe zaben gama gari a kan tikitin sabuwar jam'iyyar Patriotic Party na wannan mazaba. An zabe shi da kuri'u 62,048 daga cikin 82,377 da aka kada. [7] [12] Wannan yayi daidai da kashi 75.32% na jimlar ƙuri'un da aka jefa. [7] [12] An zabe shi a kan Fatao Iliyasu na National Democratic Congress, Zacharia Awuah na Jam'iyyar Progressive People's Party da Edward JB Danquah dan takara mai zaman kansa. [7] [12] Wadannan sun samu kuri'u 17,521, 1,284 da 1,524 na jimillar kuri'un da aka kada. [12] [7] Wadannan sun yi daidai da 21.27%, 1.56% da 1.85% na jimillar kuri'un da aka kada. [12] [7]

Rayuwa ta sirri

gyara sashe

Frimpong Kirista ne. Shi Seventh-Day Adventist ne. [1] Yana da aure da ‘ya’ya goma. [1] [2]

Duba kuma

gyara sashe
  • Jerin sunayen 'yan majalisar da aka zaba a zaben majalisar dokokin Ghana na shekara ta 2004
  • Jerin sunayen 'yan majalisar da aka zaba a zaben 'yan majalisar dokokin Ghana na 2008
  • Jerin sunayen 'yan majalisar da aka zaba a zaben 'yan majalisar dokokin Ghana na 2012

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.00 1.01 1.02 1.03 1.04 1.05 1.06 1.07 1.08 1.09 1.10 1.11 1.12 1.13 "Ghana MPs – MP Details – Frimpong, Kofi" . 6 May 2016. Archived from the original on 6 May 2016. Retrieved 2 August 2020.Empty citation (help)
  2. 2.00 2.01 2.02 2.03 2.04 2.05 2.06 2.07 2.08 2.09 2.10 2.11 "Ghana MPs – MP Details – Frimpong, Kofi" . 2 April 2016. Archived from the original on 25 April 2016. Retrieved 2 August 2020.Empty citation (help)
  3. 3.0 3.1 3.2 3.3 3.4 3.5 3.6 3.7 3.8 Peace FM. "Ghana Election 2004 Results – Kwabre East Constituency" . Ghana Elections – Peace FM . Retrieved 2 August 2020.Empty citation (help)
  4. 4.0 4.1 4.2 4.3 4.4 4.5 4.6 4.7 4.8 Elections 2004; Ghana's Parliamentary and Presidential Elections . Accra: Electoral Commission of Ghana; Friedrich Ebert Stiftung. 2005. p. 124.Empty citation (help)
  5. 5.0 5.1 5.2 5.3 5.4 5.5 5.6 Peace FM. "Ghana Election 2008 Results - Kwabre East Constituency" . Ghana Elections – Peace FM . Retrieved 2 August 2020.Empty citation (help)
  6. 6.0 6.1 6.2 6.3 6.4 6.5 6.6 Ghana Elections 2008 . Ghana: Friedrich Ebert Stiftung. 2010. p. 62.Empty citation (help)
  7. 7.0 7.1 7.2 7.3 7.4 7.5 7.6 Elections 2012 . Ghana: Friedrich Ebert Stiftung. p. 134.Empty citation (help)
  8. "Ghana MPs - MP Details - Frimpong, Kofi" . www.ghanamps.com . Retrieved 2 February 2020.
  9. Peace FM. "Kofi Frimpong Storms Parliament" . www.peacefmonline.com . Retrieved 2 February 2020.
  10. "Kofi Frimpong re-elected NPP parliamentary candidate for Kwabre East" . www.ghanaweb.com . Retrieved 2 February 2020.
  11. "Ghana MPs – MP Details – Frimpong, Kofi" . 6 May 2016. Archived from the original on 6 May 2016. Retrieved 8 July 2020.
  12. 12.0 12.1 12.2 12.3 12.4 12.5 12.6 Peace FM. "Ghana Election 2012 Results – Kwabre East Constituency" . Ghana Elections – Peace FM . Retrieved 2 August 2020.Empty citation (help)
  13. "Statistics of Presidential and Parliamentary Election Results" . Fact Check Ghana . 1 August 2016. Retrieved 2 August 2020.
  14. Peace FM. "Ghana Election 2004 Results – President" . Ghana Elections – Peace FM . Retrieved 2 August 2020.
  15. Peace FM. "Ghana Election 2008 Results – Ashanti Region" . Ghana Elections – Peace FM . Retrieved 2 August 2020.
  16. Peace FM. "Ghana Election 2008" . Ghana Elections – Peace FM . Retrieved 2 August 2020.