Harin bam a Konduga, 2018
A ranar Juma'a 16 ga watan Fabrairu 2018, an kai harin ƙuna baƙin wake sau uku a Konduga, jihar Borno, arewa maso gabashin Najeriya.[1]
Harin bam a Konduga, 2018 | ||||
---|---|---|---|---|
suicide bombing (en) | ||||
Bayanai | ||||
Kwanan wata | 16 ga Faburairu, 2018 | |||
Wuri | ||||
|
Lamarin
gyara sasheWasu ‘yan ƙuna baƙin wake biyu sun tayar da bama-baman da ke jikinsu a wata kasuwar kifi mai cike da cunkoson jama’a da misalin karfe 8:30 na dare.[1] Mintuna huɗu bayan haka, bam na uku ya tashi a kusa da wurin.
Hare-haren sun kashe tsakanin mutane 17[2] zuwa 22[1] tare da jikkata tsakanin 22 [2] zuwa 70.[3] Ɗaya daga cikin maharan mace ce, yayin da sauran biyun kuma maza ne. An kai waɗanda suka jikkata a harin zuwa asibiti a birnin Maiduguri.[2]
Bayan harin
gyara sasheBa a samu labarin lamarin ba, har sai washegari.[4] Babu wanda ya ɗauki alhakin kai harin, amma mayakan Boko Haram sun sha kai manyan hare-hare a Konduga a baya (ciki har da kisan kiyashi a watan Janairu da Fabrairun 2014 ) da kuma (ciki har da harin kunar bakin wake sau uku a watan Yunin 2019 ).[1]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 1.3 AFP. "Trio of suicide bombers kill 19 in northeast Nigeria". www.timesofisrael.com (in Turanci). Retrieved 2020-07-03.
- ↑ 2.0 2.1 2.2 "Police confirm 18 killed, 22 wounded in multiple bomb blast in Borno". TODAY (in Turanci). 2018-02-17. Archived from the original on 2020-09-11. Retrieved 2020-07-03.
- ↑ "Nigeria: three suicide bombers kill at least 20 people at market". The Guardian (in Turanci). Maiduguri. 2018-02-17. ISSN 0261-3077. Retrieved 2020-07-03.
- ↑ "Nigeria: Suicide bomb blast kill at least 18 for Konduga, Borno". BBC News Pidgin (in Pidgin na Najeriya). British Broadcasting Corporation. Retrieved 2020-07-03.