Khadijeh Saqafi
Khadijeh Saqafi (an haife ta a shekara ta 1916.- 21 ga watan Maris din Shekarar 2009) ( Persian , wanda akewa laƙabi da Qudus din Iran ita ce matar Ruhollah Khomeini, shugaban juyin juya halin Iran na shekara ta 1979.
Khadijeh Saqafi | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Tehran, |
ƙasa | Iran |
Mazauni | Tehran |
Mutuwa | Tehran, 21 ga Maris, 2009 |
Makwanci | Behesht-e Zahra (en) |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama | Khomeini 3 ga Yuni, 1989) |
Yara |
view
|
Karatu | |
Harsuna | Farisawa |
Sana'a | |
Sana'a | revolutionary (en) |
Imani | |
Addini | Shi'a |
Rayuwar farko
gyara sasheSaqafi ɗiya ce ga Haj Mirza Mohammad Saqafi Tehrani babban malami mai daraja. Haj Mirza Mohammad Saqafi jikan Agha Mirza Abolghassem Kalantar, magajin garin Tehran a ƙarƙashin Qajars a tsakiyar karni na sha tara.
Saqafi ya auri Ruhollah Khomeini a shekarar 1929, lokacin tana da shekaru 13 Ta haifi yara bakwai tare da Khomeini yayin rayuwarta, kodayake biyar kawai suka rayu tun suna yara. Danta, Mostafa, ya rasu a Iraki a shekarar 1977, yayin da na biyu, Ahmad, ya mutu sakamakon bugun zuciya a 1995 yana da shekara 49.
An bayyana Saqafi, wacce galibi ba ta fita daga idanun jama'ar Iran ba, an bayyana ta a matsayin babbar mai goyon bayan adawar mijinta ga Shah na Iran. Tsohon shugaban kasar Iran Akbar Hashemi Rafsanjani, ya ambaci Saqafi a matsayin "makusanciya kuma mafi hakuri" ga mijinta.
Mutuwa
gyara sasheSaqafi ta rasu a ranar 21 ga Maris 2009, a Tehran bayan doguwar rashin lafiya tana da shekaru 93. Dubun-dubatar mutane ne suka halarci jana’izarta, ciki har da Jagoran Iran Ali Khamenei da na lokacin Shugaba Mahmud Ahmadinejad. An binne Saqafi kusa da mijinta a kabarinsa da ke Behesht-e Zahra. Ta bar ƴaƴa mata uku, Zahra, Sadiqeh, da Farideh.