Kogin Katsina Ala
Katsina Ala (ko Katsina-Ala) kogi ne a tsakiyar Nijeriya, wanda ke tsakiyar yankinsa na Tsakiya . yana aiki a matsayin babbar mashigar Kogin Benuwai a Nijeriya. Tushen kogin an same shi ne a tsaunukan Bamenda da ke arewa maso yammacin Kamaru . Yana gudana 320 kilometres (200 mi) arewa maso yamma a Kamaru, ya tsallaka kan iyakar Najeriya da Kamaru zuwa Najeriya. [1]
Kogin Katsina Ala | |
---|---|
General information | |
Height above mean sea level (en) | 0 m |
Tsawo | 320 km |
Labarin ƙasa | |
Tsarin Daidaiton Labarin Kasa | 7°47′57″N 8°52′32″E / 7.7992°N 8.8756°E |
Kasa | Kameru da Najeriya |
Territory | Afirka ta Yamma |
Hydrography (en) | |
Watershed area (en) | 22,000 km² |
Ruwan ruwa | Niger Basin (en) |
River mouth (en) | Benue |
Sanadi | heavy metal (en) |
Wuri
gyara sasheAna samun kogin Katsina Ala galibi a jihar Benuwe ta Najeriya, bayan ya tsallaka kan iyaka tsakanin Najeriya da Kamaru, kafin ya zubar da abin da ke cikinsa zuwa Kogin Benuwai.
Garuruwa
gyara sasheKatsina-Ala babban birni ne kuma babban gari na karamar hukumar Katsina Ala a jihar Benuwai, Najeriya. Ana samun sa a bakin kogin Katsina Ala tare da ƙauyuka da yawa a kan hanyar. Tana da babbar kasuwa da ke ci a kowane Alhamis ɗin mako.
Manazarta
gyara sashe
- ↑ "Katsina Ala River | river, western Africa". Encyclopedia Britannica (in Turanci). Retrieved 2020-02-09.