Justus Akinbayo Akinsanya, FRCN (31 Disamba, 1936 – 11 Agusta , 2005) ma'aikacin jinya ne, masani a fannin ilimin halittu, ma'aikacin jinya, malami kuma mai bincike.

Justus A. Akinsanya
Rayuwa
Haihuwa Okun-Owa (en) Fassara, 31 Disamba 1936
ƙasa Birtaniya
Mutuwa 11 ga Augusta, 2005
Yanayin mutuwa  (infectious disease (en) Fassara)
Karatu
Makaranta University of London (en) Fassara
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a nurse (en) Fassara da biologist (en) Fassara
Employers Anglia Ruskin University (en) Fassara
Bournemouth University (en) Fassara
Kyaututtuka

Rayuwar farko da aiki

gyara sashe

An haife shi a Okun-Owa, Ijebu, Nigeria (kusa da Legas), Akinsanya ya cancanta a shekarar 1960 a aikin jinya, Tare da ƙwarewa a fannin cutar tarin fuka. A cikin shekarar 1967 ya yi kwasa-kwasan bayan yin rajista a fannin likitancin kasusuwa, dermatological da taɓin hankali (orthopaedic, dermatological and psychiatric). Ya shiga Jami'ar Landan inda ya sami digiri na BSc (Hons) a Human Biology sannan ya yi digiri na uku.

Akinsanya ya haɓaka samfurin Akinsanya na bionursing (1985), wanda ya bayyana a matsayin aikin jinya wanda ke amfani da shi a aikace ƙa'idodin kimiyyar halitta kamar ilmin halittu.[1]

Ya riƙe muƙamai a matsayin malami, gudanarwa da bincike, ciki har da zama malami a Cibiyar Gudanarwa da Fasaha da ke Enugu daga shekarun 1976 zuwa 1977, kafin ya zama Reader sannan ya zama Farfesa kuma Shugaban Sashin Binciken Kiwon Lafiya a Cibiyar Dorset, yanzu a jami'ar Bournemouth daga shekarun 1985 zuwa 1989.

Daga baya ya ɗauki matsayin Dean na sabuwar Faculty of Health and Social Work a Anglia Polytechnic University daga shekarun 1989 har zuwa 1996, inda matarsa, Cynthia, take aiki a matsayin malama a pre-registration nursing.[2]

An naɗa shi Farfesa Emeritus a lokacin ritaya a shekarar 1996, sannan ya ba da lokacinsa ga ayyukan agaji na Disability Croydon, Asusun jinya ga ma'aikatan jinya da Majalisar Dattawan Najeriya (Disability Croydon, Nurses Fund for Nurses and the Nigerian Council of Elders), kuma ya yi aiki a matsayin a hukumar ilimi ta gida (LEA) mai kula da makarantu biyu a Croydon.

Rayuwa ta sirri

gyara sashe

Ya taɓa shiga majalisar kula da ma’aikatan jinya ta Najeriya kuma an mai da shi ma’aikacin UK Royal College of Nursing (FRCN) a shekarar 1988.[3]

Ya rasu ne a Landan yana da shekaru 68 bayan ya kamu da cuta a taron majalisar ma'aikatan jinya na ƙasa da ƙasa da aka gudanar a Taiwan wasu watannin baya.

Manazarta

gyara sashe
  1. "Professor Justus A Akinsanya". Royal College of Nursing, Fellows. Archived from the original on 2007-10-22. Retrieved 2006-10-20.
  2. Akinsanya, Justus; Akinsanya, Justus A (1990-10-31). "Future hiding in the present". Nursing Standard. 5 (6): 13–15. doi:10.7748/ns.5.6.13.s69. ISSN 0029-6570. PMID 2124890.
  3. "RCN Fellows and Honorary Fellows". Royal College of Nursing. Retrieved 7 Nov 2022.