Julie Braun-Vogelstein
Julie Braun-Vogelstein (shekara ta 1883 – shekara ta 1971) ƴar asalin ƙasar Jamus ce ƴar tarihin fasaha, marubuciya, edita, kuma yar jarida.
Julie Braun-Vogelstein | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Szczecin (en) , 26 ga Janairu, 1883 |
ƙasa | Jamus |
Mutuwa | New York, 6 ga Faburairu, 1971 |
Karatu | |
Harsuna |
Jamusanci Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | marubuci, ɗan jarida da art historian (en) |
Tarihin Rayuwarta
gyara sasheAn haife ta a Stettin a Jamus (yanzu Szczecin, Poland). Julie Vogelstein 'yar rabbi ce Heinemann Vogelstein kuma 'yar'uwar rabbi de: Hermann Vogelstein, da masana'antu Ludwig Vogelstein da de: Theodor Vogelstein . Ta karanci tarihin fasaha da ilimin da kimiyya a Jami'ar Munich da Jami'ar Berlin . Ashekara ta 1919 ta sami digirinta na uku daga Jami'ar Heidelberg . A shekara ta 1935 tabar kasar Jamus zuwa Faransa daga baya Amurka. A shekara ta 1936 tatafi California, kuma ta zauna a Karmel daga lokaci zuwa lokaci bayan haka. Ta kasance memba na hukumar Leo Baeck Institute .
Itace sakatariyar Heinrich Braun a shekara ta (1854-1927), kuma ta zama matarsa ta biyu bayan mutuwar matarsa Lily Braun (1865-1916).Itace kuma editan Ayyukan Tattara Lily Braun.
Ta rubuta kuma ta gyara littattafai da yawa; misali ta rubuta Art: The Image of West shekara ta (1952) kuma tabuga The Diary of Otto Braun shekara ta (1924). Otto Braun shi ne angonta, wanda ta mutu ayakin duniya na daya . [1]
Mijinta ya rasu a shekara ta 1927; basu da 'ya'ya. Braun-Vogelstein ta mutu abirnin New York. [2] An gudanar da ayyuka a Riverside Memorial Chapel . [2]