Josephine Piyo
Josephine Chundung Piyo (an haife ta a shekara ta 1957) ƴar siyasar Najeriya ce wadda ta take riƙe muƙamin mataimakiyar gwamnan jihar Filato a halin yanzu.[1][2] Kafin ta zamo mataimakiyar Gwamnan jihar Filato, an zaɓeta a matsayin ƴar Majalisa a Majalisar dDokoki ta Jihar Filato.
Josephine Piyo | |||
---|---|---|---|
2023 - | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Barkin Ladi, 1957 (66/67 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Karatu | |||
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa, nurse (en) da mai karantarwa | ||
Imani | |||
Addini | Kiristanci | ||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Tasowa
gyara sashePiyo ta fito ne daga ƙaramar hukumar Barkin Ladi, An haife ta a shekara ta 1957. Haifaffiyar garin Barkin Ladi, Jihar Filato.
Aiki
gyara sasheTayi aiki a matsayin ma'aikaciyar jinya, haka ita Malama ce kafin ta shiga harkar siyasa. A cikin shekara ta1999 an zaɓe ta a matsayin ƴar Majalisar Dokokin Jihar Filato. Piyo ta riƙe matsayin mai ba gwamnan jihar Filato shawara ta musamman, daga shekara ta 2008 zuwa 2011. Har ila yau a cikin shekara ta 2018, ta zama shugabar ƙaramar hukumar Riyom, jihar Filato.
Manazarta
gyara sashe- ↑ "2023: Plateau PDP Guber Candidate Picks Female Running Mate – This Day Live". thisdaylive.com. Retrieved 2023-04-19.
- ↑ YarKarkara, Sawabiya (2022-06-21). "Plateau Governorship:Mutfwang picks a Female Lawmaker of the 4th Assembly as Running Mate". Sawabiya News. Archived from the original on 2023-04-19. Retrieved 2023-04-19.