Kaftin Josephine Okwuekeleke Tolefe (an haife ta a ranar 15 ga watan Disambar 1931 a Aniocha, jihar Delta dake Najeriya) ita ce mace ta farko da ta zama jami'in soja a Najeriya. Ita ce mace ta farko a soja kuma mace ta farko da ta kai matsayin Kaftin Sojoji a Najeriya.[1][2]

Josephine Okwuekeleke Tolefe
second lieutenant (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa 1931
ƙasa Najeriya
Mutuwa 2014
Karatu
Harsuna Turanci
Harshen, Ibo
Pidgin na Najeriya
Sojojin Ƙasa na Najeriya
Sana'a
Sana'a nurse (en) Fassara
Employers Sojojin Ƙasa na Najeriya

Rayuwa ta sirri da tushen ilimi

gyara sashe

An haife ta a ranar 15 ga watan Disambar 1931 a Ogwashi-Ukwu, kudancin Aniocha a Jihar Delta, Najeriya.[3] Ta halarci Kwalejin Koyar da Ungozoma, High Coombe Surrey, United Kingdom don yin karatun aikin jinya kuma ta kammala karatun digiri a matsayin ma'aikaciyar jinya mai rijista a ƙarƙashin Majalisar Ma'aikatan jinya na Ingila da Wales a cikin watan Agustan 1956.[4]

Josephine ta kasance ƙwararriyar ma’aikaciyar jinya amma ta yanke shawarar shiga aikin sojan Najeriya ne saboda yadda matan da suke sojan Ingila suke yi da kuma yadda suke kare ƙasarsu sun burge ta.[5] Bayan shiga soja, an naɗa ta a matsayin Laftanar na biyu a shekara ta 1961. Bayan shekaru biyu, an naɗa ta Kaftin Soja.

Ko da yake an yi bikin Josephine, amma ita da abokan aikinta mata sun fuskanci ƙalubale da yawa game da jinsinsu. Ta yi ritaya da son rai daga hidima a ranar 5 ga watan Fabrairun 1967 kuma ta wuce a 2014.[6]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-10-25. Retrieved 2023-03-28.
  2. https://www.nigeria70.com/nigerian_news_paper/meet_the_first_female_army_officer_in_nigeria/409662[permanent dead link]
  3. https://africadefensejournal.wordpress.com/2011/12/12/nigerias-first-female-army-captaini-carry-military-discipline-in-my-blood/
  4. https://globalsentinelng.com/tag/josephine-okwuekeleke-tolefe/[permanent dead link]
  5. https://www.vanguardngr.com/2011/12/meet-the-first-female-army-officer-in-nigeria/
  6. https://m.facebook.com/IQ4News/posts/10202702854750507?_rdr