Josephine Nambooze
Josephine Nambooze likita ce 'yar Uganda, ƙwararriya a fannin lafiyar jama'a, Malama, kuma mai binciken a fannin likitanci Ita ce farfesa a fannin kiwon lafiyar jama'a a Makarantar Kiwon Lafiyar Jama'a ta Jami'ar Makerere. Nambooze ita ce mace ta farko a Gabashin Afirka da ta cancanci zama likita a kusan shekarar 1959.[1]
Josephine Nambooze | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Nsambya (en) , 1930 (93/94 shekaru) |
ƙasa | Uganda |
Mazauni | Kampala |
Karatu | |
Makaranta |
Jami'ar Makerere Makarantar Hada Magunguna ta Jami'ar Makerere |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | likita, Malami da researcher (en) |
Employers |
Hukumar Lafiya ta Duniya Jami'ar Makerere |
Tarihi da ilimi
gyara sasheAn haifi Nambooze a Nsambya, a wani yanki na Kampala 'ya ce ga Joseph Lule, malamin makaranta, da Maria Magdalena Lule, uwar gida. Ita ce ta farko da aka haifa a gidan mai 'ya'ya goma sha uku. Ta halarci Makarantar Firamare ta St. Joseph's Nsambya, da Kwalejin Mount Saint Mary's Namagunga. Yayin da take Namagunga, ta karanci fannin kimiyya. Babu ɗakin gwaje-gwaje a makarantar a lokacin, ta karanci azuzuwan ilimin kimiyya a Kwalejin Namilyango, makarantar sakandaren maza da mata duka 25.5 kilometres (16 mi)[2] zuwa gabas da Namagunga.[1]
A tsakiyar shekarun 1950, an shigar da ita makarantar likitanci ta Jami'ar Makerere don yin karatun likitancin ɗan adam, mace ta farko a tarihin makarantar. Bayan kammala karatunta a Makerere, ta yi karatun digiri na biyu a Burtaniya da Amurka, ta koma Uganda a shekarar 1962.[3]
Ƙwarewa a fannin aiki
gyara sasheTa shiga ma’aikata a jami’ar Makerere a shekarar 1962 a matsayin malama a fannin kiwon lafiyar jama’a da lafiyar mata da yara. An ba ta alhakin kula da Cibiyar Kiwon Lafiya ta Kasangati, wurin koyarwa na Makarantar Kiwon Lafiyar Jama'a ta Jami'ar Makerere. Daga baya ta zama babbar malama, (associate) farfesa, da cikakkiyar farfesa a waɗannan fagagen. Ta kuma yi aiki a matsayin wakiliyar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a Botswana kuma a matsayin darektan tallafawa ci gaban ayyukan kiwon lafiya a ofishin yanki na WHO da ke Brazzaville, Kongo.[1]
Duba kuma
gyara sashe- Asibitin Mulago
- Asibitin Nsambya
- Ma'aikatar Lafiya ta Uganda
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 Mugagga, Robert (1 September 2012). "Prof Nambooze: Academic success that changed the region's history". Daily Monitor. Kampala. Retrieved 7 January 2016.
- ↑ Samfuri:Google maps
- ↑ Talemwa, Moses (4 April 2010). "Female professors tell their long story". The Observer (Uganda). Kampala. Archived from the original on 23 February 2016. Retrieved 7 January 2016.