John Flack (dan siyasan Burtaniya)
John Flack (an haife shi a ranar 3 ga watan Janairu shekara ta 1957)[1] ɗan siyasan Jam'iyyar Conservative ne a Biritaniya. Ya kasance memba na Majalisar Tarayyar Turai (MEP) mai wakiltar mazabar Gabashin Ingila, bayan ya rasa kujerarsa ga Jam'iyyar Brexit a Zaben EU na shekarar 2019.[2][3] Ya kasance magoyin bayan kungiyar Matsin Lamba na "Eurosceptic pressure group" ma taken Leave Means Leave.[4]
John Flack (dan siyasan Burtaniya) | |||
---|---|---|---|
28 ga Yuni, 2017 - 1 ga Yuli, 2019 ← Vicky Ford District: East of England (en) | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Romford (en) , 3 ga Janairu, 1957 (67 shekaru) | ||
ƙasa | Birtaniya | ||
Harshen uwa | Turanci | ||
Karatu | |||
Harsuna | Turanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa da ɗan kasuwa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Conservative Party (en) |
Rayuwa da aiki
gyara sasheFlack ya halarci makarantar sakandare ta Abbs Cross High School da ke Hornchurch. Ya daukaka daga matsayin mai horarwa zuwa ƙaramin abokin tarayyar kamfanin masu binciken hayar, kafin ya jagoranci kamfanonin kadarori daban-daban.[5]
Ya kuma yi aiki a matsayin majistare, daga farko matsayin mafi ƙaranta a Essex a yayin da aka nada shi a shekarar 1988. Ya yi aiki na tsawon shekaru 21 kafin aka kara masa matsayi a shekara ta 2009, domin ya iya tsayawa takarar Majalisar Tarayyar Turai da kuma guje wa duk wani ra'ayi na rikici.
Siyasa
gyara sasheFlack ya fito takara a mazabar majalisar Turai ta Northumbria a zaben shekara ta 1994 da London a zaɓen shekara ta 1999.[5] Ya tsaya takarar Enfield Southgate a babban zaben shekara ta 2001, wanda ya zo na biyu ga dan takarar Labour Stephen Twigg kusan rubanya rinjayen Labour a shekarar 1997. Ya shahara a cikin watan Fabrairu kafin zaben cewa "duk yana cikin jaka" kuma ya yi yakin neman zabe kadan bayan haka don jin dadin dan majalisar Labour mai ci.[6]
Ya kasance na 4 a jerin 'yan takarar Conservatives na yankin Gabashin Ingila a zabukan majalisar Turai a shekara ta 2009 da 2014, amma 3 Conservatives ne kawai aka zaba a kowane lokaci. Ya hau kujerar nasa a shekarar 2017 bayan da aka zabi takwararsa ta MEP Vicky Ford a matsayin 'yar majalisa a babban zaben kasa.[7]
Flack ya rike matsayi a kwamitin Majalisar Tarayyar Turai kan Ci gaban Yankin (REGI).[8] Ya yi aiki a matsayin kakakin raya yankin na jam'iyyar Conservative.[9] Ya kuma kasance mamba a madadin Kwamitin Kifi na Majalisar (PECH).[10]
Flack ƙwararren mai fafutukar walwala da jin daɗin dabbaobi ne, kuma ya shirya taron zagaye-zagaye kan matsaloli da ke gudana a kasuwanni Tarayyar Turai.[11] Ya kasance memba na Ƙungiyar Kula da Dabbobi ta Majalisar Tarayyar Turai.[12] A cikin shekarar 2019 an nada shi a matsayin Majiɓincin Gidauniyar Jin Dadin Dabbobi na Conservative Animal Welfare Foundation don amincewa da jajircewarsa na sake fasalin jindadin dabbobi.
Manazarta
gyara sashe- ↑ "John FLACK MEP". European Parliament. Retrieved 13 August 2017.
- ↑ "Key dates ahead". European Parliament. 20 May 2017. Retrieved 28 May 2019.
- ↑ "Key dates ahead". BBC News Online. British Broadcasting Corporation. 22 May 2017. Retrieved 28 May 2019.
- ↑ "Co-Chairmen - Political Advisory Board - Supporters". Leave Means Leave. Archived from the original on 24 October 2017. Retrieved 26 February 2018.
- ↑ 5.0 5.1 "Vote 2001 | Candidates | John Flack". BBC News. Retrieved 13 August 2017.
- ↑ "Vote 2001 | Results & Constituencies | Enfield Southgate". BBC News. Retrieved 13 August2017.
- ↑ "New Conservative MEP appointed for East of England". ITV News. 4 July 2017.
- ↑ "Members of the REGI Committee". European Parliament. 30 November 2017.
- ↑ "John Flack Conservative MEPs". Conservatives in the European Parliament. 30 November 2017.
- ↑ "Members of the PECH Committee". European Parliament. 30 November 2017.
- ↑ "Roundtable on fur labelling". Animal Welfare Intergroup. 27 September 2017.
- ↑ "Members of the Intergroup". Animal Welfare Intergroup. 30 November 2017.
Hanyoyin haɗi na waje
gyara sashe- Bayanan martaba a gidan yanar gizon majalisar Turai
- Yanar Gizo Archived 2021-05-12 at the Wayback Machine
- John Flack
- John Flack on Twitter