Jika Dauda Halliru
An haifi Jika Dauda Halliru a shekara ta alif ɗari tara da saba'in da shida 1976 a jihar Bauchi, Nigeria. Dan kasuwa ne kuma dan siyasa. Ya taba zama kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi kuma a yanzu haka dan majalisar dattawa ne mai wakiltar Bauchi ta tsakiya. An fi saninsa da Dokagi.[1][2]
Jika Dauda Halliru | |||||
---|---|---|---|---|---|
11 ga Yuni, 2019 - District: Bauchi Central
9 ga Yuni, 2015 - 9 ga Yuni, 2019 District: Bauchi Central | |||||
Rayuwa | |||||
Cikakken suna | Jika Dauda Haliru | ||||
Haihuwa | 1976 (47/48 shekaru) | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Karatu | |||||
Makaranta | Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna | ||||
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
Ilimi
gyara sasheYa tafi Kwalejin Tunawa da Sardauna da ke Kaduna, Jihar Kaduna ya kammala a shekara ta alif ɗari tara da casa'in da tara 1999. Daga nan ya koma Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna domin yin karatun Injiniya, kuma ya kammala a shekara ta 2003.
Harkar siyasa
gyara sasheAn zabi Jika a matsayin wakilin mazabar Darazo da Ganjuwa a majalisar wakilai ta tarayya kuma ya yi zango biyu a matsayin wakili, na farko tsakanin shekara ta 2007 da shekara ta 2011 da kuma na biyu tsakanin shekara ta 2011 da shekara ta 2015. Sannan a zaben shekara ta 2019 an zabe shi sanata bauchi ta tsakiya karkashin tutar APC.
Rayuwar mutum
gyara sasheJika musulmi ne. Yayi aure da yara.
Manazarta
gyara sashe
Rayuwansa ta mutum
gyara sasheYayi aure kuma yana da yara.
- ↑ Babah, Chinedu (2017-10-04). "JIKA, Hon Dauda Haliru". Biographical Legacy and Research Foundation (in Turanci). Retrieved 2020-02-20.
- ↑ "Hon. Jika Haliru biography, net worth, age, family, contact & picture". www.manpower.com.ng. Retrieved 2020-02-20.