Jami'ar Tarayya ta Kashere, Ataƙaice FUKashere,  jami'a ce ta jama'a da al'ada wacce take a jihar Gombe, yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.[1]

Jami'ar Tarayya , Kashere


Wuri
Map
 9°59′05″N 10°57′04″E / 9.984743°N 10.951202°E / 9.984743; 10.951202
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaJihar Gombe
Ƙaramar hukuma a NijeriyaAkko (Nijeriya)
Bayanan tarihi
2010
2011
Tsarin Siyasa
• Gwamna Umar Pate
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Wasu abun

Yanar gizo fukashere.edu.ng

Tarihi gyara sashe

Jami'a ce da aka kafa ta kwanan nan tana wani karamin gari wanda ake kira Kashere a wani yanki mai suna Pindiga, karamar hukumar Akko a jihar Gombe Najeriya.

Gwamnatin Goodluck Jonathan ne ya kafa ta a shekara ta dubu biyu da goma (2011). A matsayin daya daga cikin sababbin jami'o'in gwamnatin tarayya da aka kirkira a jihohi guda shida a Najeriya.

An kafa jami'ar ne domin kara samun ilimi da kuma tabbatar da daidaito a tsakanin dukka Jihohin Najeriya.[2]

Tsarin karatu gyara sashe

Sassa gyara sashe

Jami'ar tana gudanar da sashen illimi  wanda ake kira da (faculties) guda shida 6 da suka haɗa da;[3][4]

  1. Sashen illimi (Faculty of Education)
  2. Sashen kimiyya (Faculty of Science)
  3. Sashen baiwar dan Adam (Faculty of Arts and Humanities)
  4. Sashen illimin Noma (Faculty of Agriculture)
  5. Sashen gudanarwa (Faculty of Management Sciences)
  6. Sashen illimin zanantakewa (Faculty of Social Sciences).

Darussa gyara sashe

Wadannan su ne kwasa-kwasan da ake bayarwa a Jami’ar Tarayya ta Kashere.[5]

  • Accountancy/Accounting
  • Kimiyyar Noma da Ilimi
  • Aiwatar da Geophysics
  • Karatun Larabci
  • Biochemistry
  • Halittu
  • Gudanar da Kasuwanci
  • Chemistry
  • Nazarin Addinin Kirista
  • Kimiyyan na'urar kwamfuta
  • Ilimin tattalin arziki
  • Ilimin Tattalin Arziki da Ci Gaba
  • Ilimi da Larabci
  • Ilimi da Biology
  • Ilimin Laifuka da Nazarin Tsaro
  • Ilimi da Chemistry
  • Ilimi da Kimiyyar Kwamfuta
  • Kasuwancin kasuwanci
  • Ilimi da Tattalin Arziki
  • Ilimi da Ingilishi
  • Jagorar Ilimi da Nasiha
  • Ilimi da Geography
  • Ilimi da Hausa
  • Tarihi da Nazarin Diflomasiya
  • Ilimi da Tarihi
  • Ilimi da Hadakar Kimiyya
  • Alakar kasa da kasa
  • Ilimi da Lissafi
  • Ilimi da Physics
  • Harshen Turanci
  • Ilimi da Kimiyyar Siyasa
  • Gudanar da Ilimi da Tsare-tsare
  • Geography
  • Hausa
  • Kimiyyar Siyasa
  • Alakar kasa da kasa
  • Laburare da Kimiyyar Bayanai
  • Sadarwar Jama'a
  • Kididdiga
  • Microbiology
  • Kimiyyar Shuka
  • Zoology
  • Tattalin Arzikin Noma da Tsawaitawa
  • Ilimin aikin gona
  • Kimiyyar Dabbobi
  • Kimiyyar Kasa
  • Gudanar da Jama'a
  • Gudanar da Kasuwanci
  • Karatun Musulunci
  • Ilimin halin dan Adam

Shuwagabannin Jami'a gyara sashe

Shugaban jami’a na yanzu shi ne Farfesa Umaru A. Pate.[6] Ya gaji Farfesa Alhassan Muhammed Gani, wanda wa'adin mulkin sa na shekaru biyar ya kare a ranar 10 ga Fabrairu, 2021[7].

  • Farfesa Umaru A. Pate, 2021 - har yanzu
  • Farfesa Muhammad Alhassan Gani, 2016 - 2020
  • Farfesa Mohammed Kabiru Faruk, 2011 - 2015

Matsayi gyara sashe

Bisa ga webometrics, matsayin Jami'ar Tarayya ta Kashere na kasa;[8]

Matsayi a Duniya Matsayi a Nahiya Matsayin a Ƙasa Tasiri Budewa Nagarta
6911 177 56 6841 4325 7190

Manazarta gyara sashe

Hanyoyin haɗin waje gyara sashe

Shafin intanet na Jami'ar http://fukashere.edu.ng/ Archived 2022-12-02 at the Wayback Machine