Mutanen Jju, ko Ba̠jju ( furucin suna: Hausa ; Tyap, ƙabila ce da ake samu a yankin Middle Belt (Central) na Nijeriya . Kalmar Ba̠jju gajere ce ga "Ba̠nyet Jju" wanda kawai ke nufin "Alummar Jju" kuma ana amfani da ita wajen magana da yaren Jju da ke cikin Ka̠jju, mahaifar mutanen Jju. Ana samun su a Kudancin Jihar Kaduna, musamman a ƙaramar hukumar Kachia, Zangon Kataf, Jama’a da kuma a cikin ƙananan hukumomin Kaduna ta Kudu . Mutanen Ba̠jju kuma ana kiransu da suna "Kaje" wanda shine ma'anar sunan da aka yi amfani da shi ga al'ummar Jju da harshen Jju na manyan Hausawa waɗanda ba su iya furta sunan na Ka̠jju (ma'ana ƙasar Ba̠jju) da kyau. Mutanen Ba̠jju galibi manoma ne, mafarauta, maƙera da kuma ƙananan yan kasuwa.[1][2][3][4]

Jama'a Jju
Yankuna masu yawan jama'a
Najeriya

Manazarta gyara sashe

  1. Ibrahim, James (2007). The politics of creation of Chiefdoms in Kaduna State. p. 66.
  2. Naija, Sabi. "WHO ARE THE BAJJU PEOPLE OF CENTRAL NIGERIA?". Sabi Naija (in Turanci). Archived from the original on 2022-02-01. Retrieved 2022-02-01.
  3. Meek, C.K (1931). Tribes Studies in Northern Nigeria.
  4. Sunny, Idunwo (1999-06-05). "The Guardian News". p. 6. Missing or empty |url= (help)