Ishaya Mark Aku
Ishaya Mark Aku (ya rasu hudu 4 ga watan Mayun shekarar dubu biyu da biyu 2002) ya kasance ministan wasanni na Najeriya a majalisar ministocin shugaba Olusegun Obasanjo na farko. Ya rasu ne sanadiyyar hatsarin jirgin sama a Arewacin Najeriya.
Ishaya Mark Aku | |||
---|---|---|---|
ga Faburairu, 2001 - Mayu 2002 ← Damishi Sango (en) - Stephen Akiga → | |||
Rayuwa | |||
ƙasa | Najeriya | ||
Mutuwa | 4 Mayu 2002 | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa |
Fage
gyara sasheAn haifi Aku ne a ƙaramar hukumar Bassa dake jihar Filato ga marigayi babban sarkin masarautar Rukuba kuma ya yi aikin injiniyan ruwa. Ya shiga aikin gwamnati na jihar Filato, inda ya riƙe muƙamai daban-daban, kuma ya kasance babban sakatare lokacin da aka naɗa shi ministan wasanni. Wanda ya gabace shi a matsayin Ministan Wasanni, Damishi Sango, ɗan uwansa ne.[1]
Ministan wasanni
gyara sasheAn naɗa Aku ministan wasanni a cikin watan Fabrairun 2001.[2] Ya sake tsara hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya (NFA) ta zama ƙungiya mai cin gashin kanta wacce ba ta dogara da kuɗaɗen gwamnati ba. Ya wargaza Super Eagles, ƴan wasan ƙasar, bayan da suka yi rashin nasara a gasar cin kofin Afrika na 2002 a Mali. An naɗa shi shugaban majalisar ƙoli ta wasanni a Afirka.[1] Yin aiki tare da Cif Patrick Ekeji na Ma’aikatar Wasanni, Aku ya fara rage fifikon wasan ƙwallon ƙafa da ƙarfafa sauran wasanni.[3]
Mutuwa
gyara sasheA ranar 4 ga watan Mayun 2002, Aku na cikin fasinjoji 70 da ke cikin wani jirgin da ya yi hatsarin mintuna kaɗan bayan tashinsa a Kano. Jirgin dai ya nutse a hanci ne jim kaɗan da tashinsa, inda ya yi gardama a wasu gine-gine, inda ya kashe mutane da dama a ƙasa.[4] Jimillar waɗanda suka mutu sun haura mutun 148.[5] Aku dai yana kan hanyarsa ne daga Jos zuwa Legas domin kallon wasan sada zumunci tsakanin ƴan wasan Najeriya da na ƙasar Kenya.[6]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 https://web.archive.org/web/20051126143550/http://www.thisdayonline.com/archive/2002/05/05/20020505news04.html
- ↑ https://onlinenigeria.com/government/ministers.php
- ↑ https://www.vanguardngr.com/2010/04/sports-development-how-bio-can-benefit-from-ekeji/
- ↑ http://news.bbc.co.uk/2/hi/africa/1968300.stm
- ↑ https://www.cbsnews.com/stories/2002/05/06/world/main508150.shtml
- ↑ https://archive.ph/20120804060654/http://1and1.thisdayonline.com/archive/2002/05/11/20020511cov03.html