Hamma Isah Misau (an haife shi 1970 a Jihar Bauchi, Najeriya) ɗan siyasar Najeriya ne. Tsohon sanata daga Bauchi ta tsakiya shine tsohon shugaban kwamitin majalisar dattijai a kan Navy na Najeriya. [1][2]

Isah Misau
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

6 ga Yuni, 2015 -
District: Bauchi Central
Rayuwa
Haihuwa 1970 (53/54 shekaru)
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress

Misau yayi karatu a babbar Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya, Kaduna inda yayi karatu kuma ya samu digiri a harkar Kasuwanci a 1997. A shekara ta 2010, ya samu digiri na biyu a fannin aikin lauya daga Jami’ar Ahmadu Bello.

Isah Misau ya fara aikinsa ne a shekarar 2000 a matsayin jami'in Gudanarwa a rundunar 'yan sanda ta Nijeriya sannan ya yi aiki a rundunar har tsawon shekaru goma kafin ya yi murabus. A shekarar 2015, Misau ya bayyana aniyarsa ta neman takarar kujerar sanata mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya sannan ya lashe zaben a watan Maris din 2015, inda ya kayar da tsohon Mataimakin Shugaban masu rinjaye Abdul Ningi. [3][4][5]

Manazarta

gyara sashe
  1. "National Assembly is supreme, they should respect us - Sen. Isah Misau - Vanguard News". Vanguardngr.com. Retrieved 2020-01-08.
  2. "National Assembly | Federal Republic of Nigeria". Nass.gov.ng. Retrieved 2020-01-08.
  3. http://dailypost.ng/2015/03/31/senate-leader-defeated-in-bauchi-as-saraki-wins-in-kwara/
  4. 6:17 pm (2015-09-29). "Full list of 83 senators who passed vote of confidence on Saraki - Vanguard News". Vanguardngr.com. Retrieved 2020-01-08.
  5. "Angry Youths Attack Pro-Saraki Senator Isah Misau In Bauchi". Sahara Reporters. 2016-04-18. Retrieved 2020-01-08.