Isaac Kyale Kwallu an haife shi 29 Yuni 1974 ɗan kasuwan Najeriya ne kuma ɗan siyasa. Dan Majalisar Wakilan Tarayyar Najeriya ne mai wakiltar mazabar Mikang/Qua’an-Pan/Shendam na jihar Filato a majalisar wakilai ta kasa ta 10.

Kwallu ya kasance shugaban karamar hukumar Qua’an-pan ta jihar Filato a karkashin jam’iyyar APC. Majalisar dokoki ta mutum 16 na karamar hukumar Qua'an-Pan ta tsige shi daga bisani majalisar dokokin jihar Filato ta dakatar da shi. Babban kotun Jos ne ya mayar da shi bakin aiki.

A zaben 2023, ya lashe zaben wakiltar mazabar tarayya ta Mikang/Qua’an-Pan/Shendam a majalisar wakilai ta tarayya a karkashin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP). An kalubalanci zabensa a kotun sauraron kararrakin zabe da abokin hamayyarsa Hon John Dafaan na jam’iyyar All Progressive Congress amma kotun ta tabbatar da Kwallu a matsayin wanda aka zaba. Daga baya kotun daukaka kara a hukuncin da ta yanke ta soke zaben tare da goyon bayan Hon. John Dafaan.

Manazarta

gyara sashe

[1] [2]

  1. YAKUB, ABDULRASHEED (2023-03-07). "INEC releases full list of elected lawmakers for Nigeria's 10th Assembly". Peoples Gazette. Retrieved 2023-07-02.
  2. "Breaking : Quan Pan LGC Chairman Impeached". Daybreak, Politics, Entertainment, Sport. 2020-08-05. Retrieved 2023-07-12.