Isa Mohammed Bagudu
Isa Mohammed Bagudu (an haife shi a shekarar 1948) ɗan siyasan Nijeriya ne wanda aka zaɓa zuwa Majalisar Dattawan Nijeriya don ya wakilci yankin Neja ta Kudu a watan Afrilun 1999, kuma aka sake zaɓen sa a watan Afrilun 2003.
Isa Mohammed Bagudu | |||
---|---|---|---|
29 Mayu 1999 - 29 Mayu 2007 - Zainab Abdulkadir Kure → District: Gundumar Sanatan Neja ta Kudu | |||
Rayuwa | |||
Cikakken suna | Isa Mohammed | ||
Haihuwa | 1948 | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Mutuwa | 5 Mayu 2007 | ||
Karatu | |||
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Tarihin Rayuwa
gyara sasheAn haife shi a shekarar 1948 na asalin Nupe, mahaifinsa Waziri Bagudu ya kasance memba na Hukumar Kula da Karamar Hukumar ta Ibadan a cikin shekarun 1950. Bagudu ya halarci kwalejin Ansarudeen, Isolo. Ya kasance darakta a NICON daga 1991 zuwa 1993.
Harkar Siyasa
gyara sasheAn zabi Bagudu ne a mazabar dan majalisar dattijan Neja ta Kudu ta jihar Neja a karkashin jam'iyyar PDP a watan Afrilun 1999 a farkon Jamhuriya ta Hudu ta Najeriya . An nada shi mataimakin shugaban kwamitin asusun ajiyar jama'a a watan Oktoba na shekarata 2004, yayi ƙaurin suna sosai a lokacin da ya mari 'yar uwansa sanata Mrs Iyabo Anisulowo, shugabar kwamitin Majalisar Dattawa kan harkokin Jiha da Kananan Hukumomi, a wajen zauren Majalisar Tarayya. A lokacin faruwar lamarin jaridar Guardian ta ruwaito cewa rikicin nasu na iya kasancewa yana da nasaba ne da fitar da kudaden kwamitin. Sakamakon hakan Majalisar Dattawa ta dakatar da shi na tsawon makonni biyu.
Manazarta
gyara sashe