Insakulofidiya
Vergleich Wikipedia Brockhaus 2011-07 Athen.png
literary genre
subclass ofreference work, knowledge organization system, tertiary source, serial Gyara
ISOCAT id103 Gyara

Insakulofidiya ko a harshen Turanci Encyclopedia ko kuma Encyclopaedia (daga ye kalmomin harshen Girka ἐγκύκλιος παιδεία), wata hadakar bayanaice a rubuce (mafiyawanci littafi ne) ko kuma a shafukan yanar gizo. Wato dai akance Kamus ne amma shi ya kunshi cikakkun bayanai na kalma ko suna kuma a jere harafi bayan harafi.

Jadawalin jerin littattafai akan tsarin insakulofidiya
majalisar yaran a kasashen turai a insakulofidiya

Asalin Insakulofiya bugaggune a litattafa har zuwa farkon karni na 20 lokacin da aka fara saka wasu a faifayen CD da kuma a yanar gizo. Insakulofidiya ta karni na 21 mafiyawanci tafi a shafukan yanar gizo ne. Babban shafin yanar gizo daya kunshi Insakulofidiya shine shafin Wikipedia musamman ma dai na Turanci wanda yake da sama da makaloli miliyan 5, saidai shima shafin Wikipedia na Hausa shine babban shafin Insakulofidiya na Hausa na yanar gizo. Babban littafi wanda aka wallafa a na Insakulofifiya a duniya shine littafin Britannica, wasu yarurrukan suna da rubutattun litattafai na Insakulofidiya wasu kuma babu.

An wallafa dubban litattafa wadanda suka kunshi cikakkun ilimai a dubban shekaru da suka gabata. Sananne cikin litattafan farko farko akwai Trihin halittar Allah na Felin Tsoho. Sunan Encyclopedia ya samo asali ne tun a karni na 16 ma'anar sa (cikakken ilimi). Littafin Encyclopédie (da Faransanci) na Denis Diderot shine littafin Insakulofidiya na farko da mutane da dama suka hadu wajen rubuta shi.