Independence House, Ginin ofishi ne mai hawa 25, wannan ginin na dogon lokaci yana yamma da dandalin Tafawa Balewa, Onikan Legas.[1]

Independence House
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin Najeriyajahar Lagos
BirniLagos,
Coordinates 6°27′N 3°24′E / 6.45°N 3.4°E / 6.45; 3.4
Map
History and use
Opening1961
Karatun Gine-gine
Tsawo 103 m
Floors 23


Gwamnatin Birtaniya ce ta kaddamar da aikin a matsayin shaida da kuma kyakkyawan fata na goyon bayan samun ‘yancin kai a shekarar 1960.[2]

Ginin an gina shi ne da siminti mai karfi, ginin ya kunshi manyan kamfanoni da kuma hedikwatar tsaro a karkashin gwamnatin Babangida wanda aka fi sani da Defence House. A shekarar 1993, wasu sassansa sun kama wuta kuma tun bayan faruwar lamarin, ba a gudanar da ginin yadda ya kamata ba.[3]

Manazarta

gyara sashe
  1. John Alfred Williams (1962). Africa: Her History, Lands and People: Told with Pictures (Cooper Square pictorial paperback series) . Rowman & Littlefield. p. 110. ISBN 978-0-815-4025-89
  2. Nkanga, Peter. "The Starting Point". Souvenir of A Monument.
  3. Nkanga, Peter. "The Starting Point" . Souvenir of A Monument.